Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce ƙasar ta samu gagarumin ci gaba tun bayan samun yancin kai a 1960.
Yayin wani jawabi da ya gabatar wa ƙasar albarkacin cikar Najeriya shekara 65 da samun yancin kai, Shugaba Tinubu ya ce ƙasar ta samun ɓunkasa a fannin tattalin arziki da ci gaban zamantakewa da fannin ilimi.
”…dole ne a yaba wa ci gaban da ƙasarmu da samu. A yau Najeriya ta samu wadatuwar fannonin ilimi da kiwon lafiya fiye da lokacin da muka samu yancin kai”, in ji shi.
Shugaban na Najeriya ya ce a lokacin da ƙasar ta samu yancin kai a 1960, makarantun sakandire 120 ne a faɗin ƙasar, da ɗaliban da ba su wuce 130,000 ba.
“Amma bisa alƙaluman da muke da su a 2024, akwai makarantun sakandire fiye da 23,000 a ƙasarmu”, in ji.
Haka ma ya ce a lokacin da ƙasar ta samu ƴancin kai Jami’ar Ibadan da Kwalejin Fasaha da ke Yaba ne kawai manyan makarantu a ƙasar, amma bisa alƙaluman 2024 akwai jami’o’i 274 da kwalejojin fasaha 183 da kwalejojin ilimi 236 a faɗin ƙasar, yana mai cewa wannan adadi ya ƙunshi na gwamnatin tarayya da na jihohi da ma masu zaman kansu.
