Gwamna Dauda Lawal ya tabbatar wa masu zuba jari na duniya cewa jihar Zamfara ƙofa a buɗe take ga masu son zuba jari.
A jawabinsa ga masu zuba jari a taron AfSNET na biyar da aka gudanar a ranar Asabar a Algiers, Aljeriya, Gwamna Lawal ya jaddada cewa gwamnatinsa ta ɗauki aniyar sauya labarin Zamfara daga ƙalubale zuwa wani babban damammaki da jajircewa.
Lawal ya kuma bayyana cewa Zamfara tana da albarkatun ƙasa masu yawa, ba kawai zinare ba, har ma da tagulla, lithium, tantalite, da kuma granite, wanda ba a taɓa su ba.
Ya kuma bayyana cewa jihar tana kan hanyar samun irin yarjejeniyoyin zuba jari kamar na jihar Cross River da Afreximbank, inda yake shirin saurin haɗin gwiwa don tabbatar da Zamfara ta ci gajiyar irin waɗannan damammaki da kuma tallafin gwamnatin tarayya.
