Ƙungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa ta NARD a Najeriya na duba yiwuwar tsunduma yajin aikin gargaɗi daga gobe juma’a 12 ga watan Satumba, bayan da ta baiwa gwamnatin ƙasar wa’adin sa’o’i 24 ƙari kan wa’adin kwanaki 10 da ta bayar tun a baya wanda ke kawo ƙarshe a yanzu.
NARD ta cimma wannan mataki ne yayin taron majalisar zartaswarta a jiya Laraba, gabanin fitar da sanarwa a safiyar yau Alhamis kan yiwuwar tsunduma yajin aikin.
Wannan ne karo na 3 da ƙungiyar ke bayar da wa’adi ga gwamnatin Najeriyar da nufin samun jituwa don kaucewa tsunduma yajin aikin wanda a lokuta da dama ke kassara harkokin kiwon lafiya a sassan ƙasar.
Ko a watan Yuli, ƙungiyar ta bayar da wa’adin makwanni 3 sasantawa tsakanin shugabancinta da gwamnatin Najeriyar wadda ta gaza biyan haƙƙoƙin mambobin wannan ƙungiya kamar yadda ta bayyana.
Wasu daga cikin batutuwan da NARD ke so gwamnatin ƙasar ta yi mata akwai biyan mambobinta alawus-alawus tun na shekarar 2024 sai kuma kuɗaɗen ariyas na kashi 25 zuwa 35.
