Aƙalla Masallata 40 ƴan bindiga suka sace a wani masallachi da ke Gidan Turbe a ƙaramar hukumar tsafe ta jihar Zamfara da safiyar yau Litinin, harin da kai tsaye masu ruwa da tsaki ke ganin ya kawo ƙarshen yarjejeniyar sulhu tsakanin ƴan bindigar da mahukuntan jihar.
A baya-bayan nan ne jihohin Katsina da Zamfara suka ƙulla yarjejeniyar sulhu tsakaninsu da ƴanbindigar da suka addabi al’ummar jihohin arewa maso yammacin Najeriyar.
Masu sukar tsarin na yarjejeniyar sulhu tsakanin ƴan bindigar da mahukunta, na ganin tun farko tsagerun wanda aka bayyana su da ƴan ta’adda tun ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaba Muhammadu Buhari basu cancanci ayi sulhu da su ba face fatattakarsu don tilasta musu tsagaita wuta.
A ranar 28 ga watan Agustan 2025 ne shugabannin al’umma da ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Kurfi ta jihar Katsina suka ƙulla yarjejeniyar sulhu da nufin kawo sauƙi ga tashe-tashen hankula da ake fuskanta a jihar.
Kamar yadda jagororin da ke cikin wannan tattaunawa suka bayyana, yarjejeniyar ta taimaka matuƙa wajen rage hare-haren ƴan bindigar da kan kai tare da sacewa ko kashe mutane dama yin awon gaba da tarin shanu.
