Ƴansanda sun gayyaci shugabar ƙaramar hukumar Tudunwada bisa zargin sanya dogaran ta su harbi wasu ma’aikata
Rundunar Ƴansandan Jihar Kano ta gayyaci shugabar karamar hukumar Tudunwada, Sa’adatu Salisu, bisa zargin jagorantar ’yan daba wajen kai hari kan ma’aikatan wata masana’anta a yankin.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa ma’aikatan masana’antar mai suna Tasarrufi General Enterprise sun kai korafi zuwa rundunar ƴansanda da ke Bompai, inda suka zargi shugabar karamar hukumar, wadda kuma ita ce shugabar Kungiyar Kananan Hukumomi ta Ƙasa (ALGON) , reshen jihar Kano, da umartar ’yan daba da su kai musu hari da adduna tare da bada umarni ga odilan ɗin ta ta yi harbi.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴansandan Kano, Abdullahi Kiyawa, ya bayyana cewa an fara bincike kan lamarin tare da aika wasikun gayyata ga duk wadanda abin ya shafa, ciki har da shugabar karamar hukumar da ake zargi.
“An samu korafi a hukumance kan shugabar ALGON. An gayyaci dukkan shaidu da wacce ake zargi. Haka kuma an dawo da dogarin ta zuwa ga hedikwata domin ta bada bayanai kan lamarin,” in ji Kiyawa.
Ma’aikatan sun zargi shugabar ALGON da jagorantar ’yan daba da makamai wajen kai musu hari, tare da bayar da umarni ga dogarin ta da ta yi harbi, abin da ya jawo raunuka da dama.
Da ya ke bayyana lamarin ga jaridar nan, Suyudi Umar, manajan kamfanin, ya ce a ranar Alhamis, 28 ga watan Agusta, Sa’adatu Salisu ta je wurin kamfanin tare da injiniyan da ke aikin ginin titin Tudunwada, tana tambayarsa dalilin da yasa bai bar wurin ba.
Manajan ya zargi shugabar ALGON da nacewa dole ya dauke masana’antarsa daga wurin da take, inda take ikirarin cewa kasancewarta shugabar karamar hukuma, tana da damar yin duk abin da take so a cikin garin.
Umar ya kuma ce lokacin da injiniyan aikin ya nuna mata cewa kamfanin ba ya cikin yankin da ake aikin titin, sai ta gaggaya masa magana.
Ya kara da cewa bayan ta tafi daga wurin, sai ta dawo wajen kamfanin da misalin ƙarfe 5 na yamma tare da sama da ’yan daba 200 dauke da muggan makamai, suka fara kai hari kan ma’aikatansa.
