Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da addu’a ga Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa yana da kyakkyawar manufa ga ƙasa da ‘yan ƙasar.
Wike ya bayyana hakan a ranar Juma’a a lokacin ƙaddamar da aikin gina hanyar Arterial Road N5 mai lamba 6, wadda ake kira Obafemi Awolowo Way, a Life Camp, Abuja.
Ya ce Shugaba Tinubu yana kokarin dawo da karkashin sa a wajen mutanen da suka rasa shi ta hanyar shirinsa na “Renewed Hope Agenda.”
Wike ya jaddada cewa dukkan ayyukan da ake ci gaba da yi a babban birnin tarayya sun samo asali ne daga amincewar da Shugaba Tinubu ya da bayar, kuma ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da goyon bayan gwamnatin yanzu don cika alkawuran da aka dauka.
