Wata Ƙungiya daga arewacin Najeriya da Majalisar Matasan Arewa sun gargaɗi gwamnatin tarayya kan kafa ‘yan sandan jihohi a faɗin ƙasar, suna gargadin cewa hakan na iya kara dagula tsaro kuma za a iya amfani da su wajen siyasa.
Suna jan hankalin gwamnatin da cewa gwamnoni za su iya amfani da ‘yan sandan jihar wajen kai hari ga abokan hamayyar siyasa, musamman a gab da zaben 2027, saboda an sha ganin yadda ake amfani da ‘yan bangar siyasa a wasu jihohin.
Kungiyoyin sun ba da shawarar karfafa hukumomin tsaro na tarayya da ake da su, kamar ‘yan sandan Najeriya, ta hanyar gyare-gyare, da kawo sabon tsari game da hukumar, sannan da ingantaccen horo don magance kalubalen tsaro na kasar, maimakon kafa sabbin tsarin da za su iya zama abin siyasa.Hukumomin tsaro na jihohi, kamar yadda ake magana a Najeriya, suna nufin yiwuwar kafa ‘yan sandan jiha ko wasu rundunonin tsaro da gwamnatocin jihohi za su ke kula da su, maimakon hukumomin tsaro na tarayya kamar ‘yan sandan Najeriya.
Wannan ra’ayi ya jawo cece-kuce, inda wasu ke ganin zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro na gida, yayin da wasu, kamar Kungiyar Dattawan Ci gaba ta Arewa da Majalisar Matasan Arewa, ke jin tsoron cewa gwamnoni za su iya amfani da irin wannan rundunar a wata hanyar ta daban a siyasa.
