Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno ya tabbatar da sabon kisan da ‘yan Boko Haram suka yi, inda ya ce mutane 63 ne suka rasa rayukansu.
A ranar Asabar, Zulum ya ziyarci al’ummar Darajamal a karamar hukumar Bama don ta’aziyya ga iyalan wadanda aka kashe a daren Juma’a. Wadanda aka kashe sun hada da sojoji biyar da kuma fararen hula kusan 58.
Zulum, ya tabbatar da cewa lamarin abun takaici ne kuma abun baƙinciki, ya gana da shugabannin al’ummar wurin kuma ya jajanta wa ga iyalan da suka rasa rayukansu.
A cewarsa ga manema labarai, “Muna nan don ta’aziyya da mutanen Darajamal kan abin da ya faru a daren jiya wanda aka kashe mutane da yawa. Hakan yana da matukar bakin ciki.
“An sauya wa al’ummar yankin wuri watanni kadan da suka wuce kuma suka ci gaba da gudanar da al’amuran su na yau da kullum, amma abin takaici, sun fuskanci harin Boko Haram a daren jiya. Ziyararmu ita ce don ji musu tausayi da kuma karfafa su.” Inji gwamna Babagana Umara Zulum.
Wannan hari yana daga cikin munanan hare-haren da Boko Haram ke ci gaba da kai a Jihar Borno, wanda ke nuna ci gaba da kalubalen tsaro a yankin. Zulum ya bukaci karin tallafin soji don magance ‘yan ta’adda, yayin da yake nuna rashin jin dadinsa da sake dawowar ‘yan Boko Haram a wasu yankuna kamar Tumbus a tafkin Chadi da tsaunin Mandara a cikin dajin Sambisa.
Ya kuma ƙara jaddada cewa rashin isasshen sojoji da kuma rashin kula da iyakoki yanda ya kamata suna taimakawa wajen ci gaba da wannan ta’addancin.
“Tsaron ‘yan kasa da dukiyoyinsu dole ne ya zama babban abin da za a fi mayar da hankali a kai don magance wannan rikici mai tsanani.”
