Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ki amincewa da cewa tsohon gwamna Nasir El-Rufai shi ne jagoransa a siyasance, a maimakon haka ya lissafa Shugaba Bola Tinubu da kuma marigayi lauya mai kare hakkin bil adama Chief Gani Fawehinmi a matsayin manyan masu tasiri a kansa.
A cikin shirin TVC na *Politics on Sunday*, Gwamnan ya jaddada yadda yake mai da hankali kan samar da shugabanci mai kyau a Kaduna kuma ya ki amsa Nasir El-Rufai a matsayin mai gidan sa a siyasance.
Kuma ya ƙara da cewa dangantakarsa da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta ɗade tun shekarar 1994 a gidan Beko Ransome-Kuti, kuma ya ƙara bada misali Fawehinmi a matsayin shugaba kuma uba a siyasa lokacin gwagwarmayarsa.
A hirar tasa ya mayar da martani akan Tsohon gwamnan jihar Nasir El-Rufai akan kalaman sa da yayi na cewa yanayin shugabancin mulkin ƙasar akwai gyara.
Gwamnatin Sani ta mayar da martani ga waɗannan ikirari, inda tace maganganun da El-Rufai basu da tushe bare makama kuma sannan ya ƙara da cewa wannan maganganu na iya kawo rarrabuwar kai a faɗin jihar.
