Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa a Abuja fadar gwamnatin Najeriya ta tsunduma yajin aikin gargaɗi na kwanaki 7, da nufin tilastawa gwamnatin ƙasar aiwatar da wasu gyare-gyare a asibitocin birnin.
Wata sanarwa da shugaban ƙungiyar George Ebong ya sanyawa hannu ta ruwaito mambobi da sauran manyan shugabannin ƙungiyar na kokawa da halin da asibitoci ke ciki a Abuja, na rashin kayakin aiki da sauran tarin matsaloli.
Ko a watan jiya sai da likitocin na Abuja suka roƙi gwamnatin Najeriya ta samar da gyare-gyare a harkokin kiwon lafiyar birnin lura da manyan ƙalubalen da yake fuskanta.
Sanarwar ta ruwaito Ebong na cewa Likitoci na aiki cikin takura da ƙololuwar matsi a sassan Abuja, ta yadda da dama kan yi hatta ayyukan da basu shafe su saboda ƙarancin jami’ai dama kayakin gudanarwa.
A cewar shugaban, idan har gwamnati bata ɗauki matakan da suka kamata ba, sashen lafiyar na Abuja ka iya durƙushewa kowanne lokaci daga yanzu.
Baya ga Likitocin na Abuja su ita kanta uwar ƙungiyar Likitocin ta ƙasa na takun saƙa da gwamnatin Najeriyar kan tarin haƙƙoƙinta da mahukuntan ƙasar suka gaza biyanta baya ga rashin kayakin aiki a asibitoci.
