Shugaban rundunar sojan ruwa Ibok-Ete Ibas (mai ritaya),wanda aka bawa riƙon ƙwarya na jihar Rivers, ya sanar da cewa ayyukan binciken ma’aikata sun ceci jihar daga Almundahanar biliyan 5 daga lissafin albashi na watan Agusta ta hanyar gano da kuma cire ma’aikatan bogi da masu arin-gizo a lissafin ma’aikata.
A lokacin bikin murnar Makon Ma’aikatar Farashin shekarar 2025 a Port Harcourt, Ibas ya ce kuɗaɗen da aka dawo dasu za’a saka a cikin abubuwan more rayuwa masu mahimmanci da ayyukan zamantakewa don ci gaban da zai dawwama.
Binciken sun tabbatar da ma’aikatan jihar na gaskiya guda 37,703 a madadin lissafin da ya gabata na sama da 43,000, da ma’aikatan fansho guda 19,186 a madadin sama da 25,500, inda suka bayyana ma’aikatan bogi 5,297 da ma’aikatan fansho na bogi guda 6,314.
