Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta janye yajin aikin gargaɗi na kwana biyar da ta fara a daren ranar Juma’ar da ta gabata.
Shugaban ƙungiyar, Dakta Tope Osundara, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya aika wa jaridar Punch da ake wallafawa a ƙasar a daren ranar Asabar 13 ga watan Satumbar, inda ya umarci mambobinsu da su koma bakin aiki a wannan Lahadi.
Osundara, yace gwamnati ta biya musu wasu daga cikin buƙatunsu, tare kuma da alƙawarin duba sauran batutuwan da suke yajin aiki akan su, sai dai har kawo yanzu babu wani ƙarin bayani game da buƙatun nasu da aka biya.
Ƙungiyar ta kuma sake ba wa Gwamantin Tarayyar ƙasar wa’adin wasu makwanni biyun da ta cika alƙawarin da ta ɗauka na biya musu sauran buƙatunsu, in ba haka ba za su zunduma wani yajin aikin.
Tun a daren juma’a ne likitocin masu neman ƙwarewa suka tsunduma yajin aikin na gargaɗi, bayan ƙarewar wa’adin da ƙungiyar ta ba gwamnatin tarayya kan batutuwan da suka shafi albashi, alawus, da walwalar ma’aikata.
A baya dai, ƙungiyar likitocin masu neman ƙwarewa NARD, ta ba wa Gwamnatin Tarayyar Najeriyar, wa’adi a mabanbantan lokuta kafin shiga yajin aikin na gargaɗi a ranar Juma’a.
Da farko sun ba ta wa’adin kwanaki 21 a watan Yulin da ya gabata, suka sake ba ta wani wa’adin na kwanaki 10 wanda ya ƙare a ranar 10 watan Satumbar nan, sai kuma wa’adin sa’o’i 24 da suka sake ba wa Gwamnatin gabanin shiga yajin aikin da suka kawo ƙarshensa a wannan Lahadi.
