A Najeriyar wasu alƙaluma sun nuna sake samun sauƙin hauhawar farashi da tsadar rayuwa a sassan ƙasar cikin watan da ya gabata na Agusta, kamar yadda hukumar ƙididdiga ta NBS ke cewa a wani rahotonta na wata-wata.
A cewar NBS hauhawar farashin ta ragu daga kashi 21.88 a watan yuli zuwa kashi 20.12 a watan Agusta, yayinda kayakin masaraufi ke ci gaba da sauka.
Tuni ƴan Najeriya suka fara samun sauƙin hauhawar farashin kayakin amma waɗanda ake samarwa a cikin gida, wanda ke nuna cewa babu sauƙin kan kayakin da ake shigarwa cikin ƙasar da ke ƙetare.
An dai fi samun wannan sauƙi ne kan kayakin abinci, lamarin da ke nuna kayakin da ake nomawa a cikin gida ne suke karyawa.
Duk da cewa za a iya kallon wannan lamari a matsayin nasara amma ta gefe guda kai tsaye saukar farashin kayan abinci na gida na kassara manoma ne waɗanda suka zuba maƙuden kuɗaɗe wajen sayan kayakin noma kama daga irin shuki da kuma takin zamani.
Masana a wannan fanni na ganin wajibi ne mahukuntan ƙasar su samar da tallafi a wannan fannin don kaucewa ci gaba da durƙushewar manoman da ka iya haddasa ƙamfar abinci haɗe da tsadarsa a wannan ƙasa mafi yawan jama’a a Afrika.
