Kotu a Afrika ta kudu ta aike da wasu ƴan ƙasar China 7 gidan yari na shekaru 20 kowannensu bayan samunsu da laifin safarar mutane da kuma azabtar da su ta hanyar tilasta musu ayyukan bautarwa masu wahala.
Ƴan Chinar da suka ƙunshi Maza 4 da mata 3, tun a farkon shekarar nan ne aka kame su tare da fara tuhumarsu da wannan laifi a gaban kotun ta Afrika ta kudu gabanin tabbatar da hannunsu dumu-dumu da ya kai ga yanke musu hukuncin.
Bayanai sun ce mutanen da ƴan Chinar suka yi safararsu sun ƙunshi wasu ƴan ƙasar Malawi 91 ciki har da ƙananan yara 37.
Mahukuntan Afrika ta kudu sun ce ƴan Chinar sun killacewa waɗannan mutane a wani kamfani da ke birnin Johannesburg tare da tilasta musu ayyuka masu wahala cikin ƙasƙanci da azabtarwa.
Yan China da ke kasuwanci a Afrika ta kudu galibi sukan yi amfani ƴanciranin ƙasashen ƙetare wajen tafiyar da harkokinsu a kamfanoni lura da cewa sun fi sauƙin biya fiye da ƴan ƙasa.
Sai dai mahukuntan sun ce galibi ƴan Chinar kan azabtar da ma’aikatan nasu tare da hansu fita don ganin ƴan uwansu.
