Rukunin farko na ƴan ciranin Afrika sun isa Ghana daga Amurka, wanda ke ƙunshe da ƴan ƙasashen Najeriya da Gambia da kuma sauran yankunan yammacin Afrika.
Wannan na zuwa ne bayan da tun a jiya Laraba shugaba John Dramani Mahama na Ghanar ya sanar da shirin fara karɓar ƴan ciranin amma bisa sharaɗin kasancewarsu ƴan ƙasashen yammacin Afrika kaɗai.
Kafar labarai ta Reuters ta ruwaito cewa ƴan ciranin su 14 tuni suka sauka a birnin Accra yayin da mahukuntan ƙasar zasu taimaka wajen aikin rarrabasu zuwa ƙasashen su na asali.
Shugaba John Dramani ya bayyana cewa tun farko Amurka ce ta yi musu tayin karɓar baƙin da zata kora amma Ghana ta kafa mata hujjar cewa dole su kasance ƴan ƙasashen yammacin Afrika, kasancewar akwai yarjejeniyar rashin buƙatar biza tsakanin ƙasashen.
Amurka na ci gaba da ƙoƙarin samun ƙasashen da zasu karɓi wani kaso na ƴan cirani da baƙin hauren da suka yi mata dafifi ƙarƙashin sabbin tsare-tsaren shugaba Trump na rage yawan baƙi marasa takardun izinin zama a ƙasar.
Kuma tuni ƙasashen Rwanda da Sudan ta kudu da kuma Eswatini suka aminta da karɓar wani kaso, kodayake ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam na bayyana shakku kan tsaro da lafiyar ƴan ciranin a waɗannan ƙasashe.
