A Najeriya, an fara wata sabuwar dambarwa tsakanin ƙungiyar direbobin dakon mai da iskar gaz ta NUPENG da matatar Ɗangote, bayan da Attajirin na Afrika ya sanar da sayo motoci dubu 4 da zai yi amfani da su don rarraba man fetur a sassan ƙasar.
Wannan mataki na Ɗangote a cewar bayanai na da nufin sauƙaƙa koken jama’a na rashin samun man akan lokaci da kuma tarnaƙin da a wasu lokuta ake fuskanta daga ita wannan ƙungiya ta NUPENG wadda ita ke da alhakin rarraba albarkatun.
Sai dai yayinda NUPENG ke cewa magoya bayanta ne ke da hurumin raba mai da iskar gaz a Najeriyar saɓanin Ɗangote, masu sharhi na ganin cewa Ɗangote, na damar raba hajarsa sakamakon sakin marar da aka yi wa ɓangaren kasuwanci a ƙarƙashin dokokin wannan ƙasa.
Sai dai tuni wannan ƙungiya ta yi barazanar tsunduma yajin aiki yayinda ta samu goyon bayan ɓangarori da dama daga wannan sashe na albarkatun man fetur, ciki har da ƙungiyar masu rarraba mai da iskar gaz ta NAGOSA da kuma ta masu gidajen mai wato PETROAN kana ƙungiyar masu motocin haya ta NARTO kana ƙungiyar ma’aikatan sashen man fetur da iskar gaz.
