Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sunkai hari gidan Dr. Ifeanyi Ogbu, sanannen likitan dabbobi kuma tsohon shugaban kungiyar likitocin dabbobi ta Najeriya (NVMA) a yankin A birnin tarayya, a gundumar Kubwa da ke hanyar Kubwa-Kaduna a Abuja.
Maharan sun harbe Dr. Ogbu inda nan take ya mutu a lokacin harin, sannan suka sace yaransa uku, wadanda har yanzu ba a gano inda suke ba.
Dr. Ifeanyi Ogbu, wanda abokan aikinsa suka bayyana a matsayin kwararre a fannin likitan dabbobi ne a Abuja.
Daren Juma’a, 3 ga watan Oktoba, aka ga gawarsa,Dr. Ogbu ya mutu bayan an taba sace shi tare da yaransa na dan lokaci.
Har yanzu ba a saki yaransa ba, kuma ba a san inda suke ba.
Matar Dr. Ogbu, wadda ke shayarwa, da sauran ‘yan uwan sa sun shuga mayuwa cin lamarin da abun ya faru.
Tuni dai al’ummar likitoci da masu aikin dabbobi a Najeriya sukai Allah wadai game da kisan inda ya nuna damuwa game da tsaro a yankin.
Abokan aikin sa sun bukaci hukumomi su dauki mataki cikin gaggawa don ceto yaransa da kuma tabbatar da adalci. Kokarin jami’an tsaro da iyalan don gano inda yaransa suke ya ci gaba, tare da addu’o’i da tallafi daga abokai da kwararru.
