Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ya ce, jam’iyyar APC za ta mamaye jihohi 30 cikin 36 da ke ƙasar nan kafin shekarar 2026.
Mohammed ya bayyana haka ne a taron dabarun aiki na watanni uku-uku na shekarar 2025 na ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC wanda aka gudanar a Maidugurin jihar Borno.
Taron ya mayar da hankali kan yadda za a inganta haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohin da APC ke mulki.
Ministan kuma ya ce, yawaitar sauya sheka zuwa APC na faruwa ne saboda kyawawan manufofi da shirye-shiryen shugaba Tinubu.
Ya kuma ce, hakan ya haifar da ingantaccen mulki da gyaran tattalin arziki da daidaituwar darajar Naira.
