Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP na Arewa sun amince da tsohon Ministan Ayyuka Na Musamman Da Harkokin Gwamnati, Kabiru Tanimu Turaki, SAN, a matsayin dan takarar da suka amince da shi ya zama shugaban jam’iyyar na kasa. Hakan na zuwa ne gabanin babban taron jam’iyyar na kasa da za a gudanar a birnin Ibadan na jihar Oyo a shekarar 2025, An cimma wannan matsayar ne bayan wani gagarumin taron tuntuba da masu ruwa da tsak n jam’iyyar na Arewacin kasa suka gudanar a Abuja. A cewar majiyoyi a wurin taron, amincewar na da nufin gabatar da matsayar Arewa…
Author: EDITOR
Mai fafutukar kare hakkin dan adam kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, an kama shi a Babbar Kotun Tarayya a Abuja. Sowore, wanda ya jagoranci zanga-zangar #FreeNnamdiKanuProtest a Abuja, a ranar Litinin, ya gudu lokacin da ‘yan sanda suka kama wasu masu zanga-zangar. Daga baya ya shiga shafukan sada zumunta don sanar da kama masu zanga-zanga 13, ciki har da dan uwan Nnamdi Kanu da lauyansa. ‘Yan sanda sun gargadi wadanda ke shirin gudanar da zanga-zanga don sakin shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) da aka haramta kungiyar, cewa kada su kusanci wasu wuraren da aka hana…
Hukumar DSS ta yi gargadin shirin kungiyar ISWAP na kai hari a wasu garuruwan jihohin Ondo da Kogi. Wannan gargadin na kunshe ne a cikin takardar sirri mai kwanan wata 20 ga Oktoba, 2025, wacce aka aike wa kwamandan 32 Artillery Brigade na rundunar sojin kasar nan da ke Akure. Takardar wacce daraktan tsaro na DSS a jihar Ondo, Hi Kana, ya sanya wa hannu, ta nuna cewa an samu sahihin bayanan sirri cewa ‘yan ta’addan na shirin kai hare-hare. Hukumar ta ce ‘yan ta’addan sun fara gudanar da leƙen asiri a wadannan yankuna, tana kuma roƙon jami’an tsaro da…
Gwamnatin ihar Gombe, ta ceto yara 59 da ake zargin an yi safararsu cikin watanni takwas da suka gabata. Daraktan Hukumar Sufuri na jihar Gombe, (Gombe Line) Dakta Sani Sabo, ya bayyana hakan, yana mai cewa sun samu nasarar ne sakamakon sabon tsarin sufuri da jihar ta kafa, wanda ya haɗa dukkanin tashoshin mota a waje ɗaya domin samun tsaro mai inganci. “Haɗin gwiwar da ke tsakanin ‘Yansanda da hukumomin NDLEA da NAPTIP da NSCDC ya taimaka wajen daƙile manyan laifuka kamar safarar yara da miyagun ƙwayoyi da kuma mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba. “Mun ceto yara 59 tare…
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya bayyana salon siyasar kwakwaso na jajircewa wajen hidimar jama’a da ilimi da ci kuma gaban ƙasa na ci gaba da zama abin koyi ga al’umma daga ƙarni zuwa ƙarni. Atiku ya bayyana hakan ne a wani saƙon taya murna da ya aike ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayin da yake cika shekaru 69 a duniya. Atiku ya wallafa a sakonne a shafinsa na Facebook a ranar Litinin. “Irin gudunmawar da Sanatan ke bayarwa wajen inganta rayuwar talakawa da gina ƙasa abin yabo ne”. In ji shi. Atiku ya kuma ta ya Kwankwaso da…
Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa Hukumar EFCC ta yi nasarar tara dukiyar da ta haura naira biliyan 500 a tsawon shekaru biyu na gwamnatinsu. Shettima ya bayyana haka ne a yayin wani taron bita da ƙara wa juna sani na alƙalai da Hukumar EFCC tare da haɗin gwiwar Hukumar Shari’a ta Najeriya (NJC) suka shirya a Abuja. Shettima wanda ya wakilci Shugaba Tinubu a taron, ya buƙaci alƙalai da sauran ma’aikata a ɓangaren shari’a da su ƙara ƙaimi tare da yin aiki bisa gaskiya da adalci. “Ana fara samun matsala ne a ƙasa da zarar masu riƙe…
Hukumar Leƙen Asirin Soji ta Najeriya (DIA) tana gudanar da bincike kan wani tsohon gwamna bisa zarginsa da ɗaukar nauyin sojoji da nufin kifar da gwamnatin Tinubu. Rahotanni sun bayyana cewa, akwai zargi mai karfi cewa tsohon gwamnan, wanda ɗan asalin yankin Kudu ne kuma tsohon babban jami’in gwamnati a ɓangaren albarkatun mai da iskar gas ne, ya ɗauki nauyin yunƙurin juyin mulkin, wanda da aka shirya aiwatarwa a ranar 25 ga watan Oktoba. A ƙarshen mako ne jaridun Sahara Reporters da kuma Premium Times suka ruwaito cewa wasu hafsoshin soji 16, da Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta ce…
Gwamnatin tarayya ta ce kammala aikin sabbin gine-gine a Asibitin koyarwa na Aminu Kano, zai kara saukaka yadda al’umma ke turuwa zuwa kasashen ketare domin neman Lafiya. Mataimakin shugaban majalisar dattawan kasar nan Sanata Barau Jibrin ne bayyana hakan, a ziyarar duba wasu gine-gine da gwamnatin tarayya ke yi karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Sanata Barau Jibrin ya ce kammala ayyukan zai kara saukakawa, da kuma kawo karshen zuwa kasashen ketare domin neman lafiya. A nasa jawabin shugaban asibitin koyarwa na Aminu Kano, Farfesa Abdurahama Abba Shehe, ya ce dama asibitin na bukatar irin sabbin ayyukan wanda zai…
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya kaddamar da ƙarin sabbin jami’an tsaro guda 200 domin ƙarfafa tsaron al’umma a fadin jihar. Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Jihar ta Katsina, Malam Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar. Sanarwar ta bayyana cewa sabbin jami’an rukuni na uku ne da aka kammala basu horo, kuma za a tura su zuwa ƙananan hukumomin Kankia da Dutsinma, inda kowace za ta karɓi jami’ai guda 50. Gwamna Radda ya ce wannan mataki na daga cikin shirin gwamnatinsa na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankunan da…
Sakamakon wani bincike da hukumar NDHS ta gudanar ya nuna yadda Najeriya ta samu raguwar haife haife a shekarar da ta gabata ta 2024 zuwa kashi 4.3 cikin dari daga kashi 5.3% da kasar ke gani a baya. Wannan sakamako ya nuna canjin a alkaluman da Najeriyar ke tattarawa na yawan haihuwa a sassan kasar mafi kololuwa cikin shekaru 5 da suka gabata. Karamin ministan lafiya na Najeriyar Iziaq Salako da ke sanar da hakan yayin zaman taron kaddamar da wannan rahoto da ya gudana Abuja, ya ce Najeriya ta samu wannan raguwar haife haife ne sakamakon karuwar matan da…