Author: EDITOR

Kotu a Ghana ta zartas da hukuncin ɗaurin shekaru 96 kan wasu ƴan Najeriya 3 da aka samu da laifin satar motoci a birnin Kumasi na lardin Ashanti. Ƴan Najeriyar 3 da aka bayyana sunansu da Francis Friday da Linus Agwazie da kuma Russell Ekenze waɗanda aka kame tun a ranar 20 ga watan Yuni bayan da aka zarge su da satar motoci a wajen ajiyar ababen hawa. Kakakin ƴansandan lardin Ashanti, Godwin Ahianyo, ya ce an miƙa mutanen gaban kotu tun a ranar 22 ga watan Yuli kuma bayan fara yi musu shari’a ne aka tabbatar da laifinsu. Wannan…

Read More

A ranar 10 ga Satumba, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, karkashin jagorancin Alkali Emeka Nwite, ta ki amincewa da belin wasu mutane biyar da ake zargi da shirya harin ta’addanci a ranar 5 ga Yuni, shekarar 2022, a Cocin St. Francis Catholic Church da ke Owo, Jihar Ondo. Harin, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 40 da kuma raunatar mutane sama da 100, ya hada da wasu ‘yan bindiga dauke da bindigogin AK-47 da na’urorin fashewa (IEDs) wadanda suka kai hari a cocin a lokacin ibadar ranar Fentikos, inda suka buɗe wuta kan harbi masu ibada, sannan…

Read More

Kotun Amurka ta ɗaure wani babban jami’in NNPC kan laifin rashawa Amurka ta damƙe wani tsohon babban jami’in kamfanin mai na Najeriya Paulinus Okoronkwo bayan samunsa da laifin karɓar rashawar dala miliyan 2 da dubu 100 daga wani kamfanin mai na China. Bayanai sun ce Mr Okoronkwo ya karɓi waɗannan kuɗaɗe ne lokacin da ya ke bakin aiki a kamfanin man na Najeriya NNPC don baiwa kamfanin na China lasisin samun damar haƙar mai a cikin ƙasar ta yankin yammacin Afrika. Bayan gurfana gaban kotu a Amurkan, Mr Okoronkwo mai shekaru 58 wanda lauya ne da yanzu haka ke zaune…

Read More

Qatar ta fitar da wasu sabbin dokokin bayar da biza ga ƴan Najeriya da nufin magance matsalar zaman da ya wuce ƙa’ida a cikin ƙasar ta yankin Gulf, ciki har da sharaɗin daina baiwa maza ƴan Najeriyar izinin shiga ƙasar face suna tare da iyalansu. Wata sanarwa da gwamnatin Qatar ta fitar game da sabbin dokokin bayar da izinin shiga ƙasar ne ke bayyana wannan mataki kan ƴan Najeriya a wani yunƙuri da ƙasar ke yi don tsaftace harkokin shige da fice dai dai lokacin da ta buɗe ƙofa ga masu zuba jari da kuma ɗaukar ma’aikata daga ƙetare. Gwamnatin…

Read More

Poland ta kakkaɓo jirage marasa matuƙa da Rasha ta harba mata Poland ta sanar da harbo wasu jirage marasa matuƙi mallakin Rasha a sararin samaniyarta, karon farko da ƙasar mamba a ƙungiyar tsaro ta NATO ke ganin irin wannan takala daga Moscow, a wani yanayi da har yanzu ake ci gaba da kai ruwa rana tsakanin Ukraine da Rashan a ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙinsu na fiye da shekaru 3. Firaminista Donald Tusk ya ce wannan ce mafi ƙololuwar takala da ƙasar ke gani daga Rasha inda dakarunta suka lissafa jirage marasa matuƙa har guda 19 da suka ratsa sararin samaniyarta,…

Read More

Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) ya bukaci Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da ya tabbatar da bin kundin tsarin mulkin Najeriya ta hanyar maido da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ba tare da ɓata lokaci ba. SERAP ta bayyana cewa shafe watanni shida da aka yi wa Sanata Natasha ba bisa ka’ida ba ne saboda ya dogara ne kawai a kan amfani da ‘yancinta na faɗar albarkacin bakinta, wanda ke da kariya a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (kamar yadda aka gyara) da kuma yarjejeniyoyin haƙƙin ɗan adam na duniya kamar su Sashe na 39 na Kundin Tsarin Mulkin…

Read More

Gwamna Dauda Lawal ya tabbatar wa masu zuba jari na duniya cewa jihar Zamfara ƙofa a buɗe take ga masu son zuba jari. A jawabinsa ga masu zuba jari a taron AfSNET na biyar da aka gudanar a ranar Asabar a Algiers, Aljeriya, Gwamna Lawal ya jaddada cewa gwamnatinsa ta ɗauki aniyar sauya labarin Zamfara daga ƙalubale zuwa wani babban damammaki da jajircewa. Lawal ya kuma bayyana cewa Zamfara tana da albarkatun ƙasa masu yawa, ba kawai zinare ba, har ma da tagulla, lithium, tantalite, da kuma granite, wanda ba a taɓa su ba. Ya kuma bayyana cewa jihar tana…

Read More

Shugaban rundunar sojan ruwa Ibok-Ete Ibas (mai ritaya),wanda aka bawa riƙon ƙwarya na jihar Rivers, ya sanar da cewa ayyukan binciken ma’aikata sun ceci jihar daga Almundahanar biliyan 5 daga lissafin albashi na watan Agusta ta hanyar gano da kuma cire ma’aikatan bogi da masu arin-gizo a lissafin ma’aikata. A lokacin bikin murnar Makon Ma’aikatar Farashin shekarar 2025 a Port Harcourt, Ibas ya ce kuɗaɗen da aka dawo dasu za’a saka a cikin abubuwan more rayuwa masu mahimmanci da ayyukan zamantakewa don ci gaban da zai dawwama. Binciken sun tabbatar da ma’aikatan jihar na gaskiya guda 37,703 a madadin lissafin…

Read More

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Oyo ta sanar da ceto wani ɗan ƙasar Masar da aka sace a safiyar ranar 8 ga Satumba, yankin Alomaja da ke Idi-Ayunre, Ibadan. A cewar kakakin rundunar, CSP Adewale Osifeso, Rundunar ƴansandan ta ceto wanda aka sace cikin sa’o’i 24 ba tare da an biya kuɗin fansa ba. Ayyukan ceto ya haɗa da jami’an 4 PMF Ibadan, ƙwararrun ƙungiyar leƙen asiri da dabaru, tare da ‘yan banga na gida da kuma haɗin gwiwa da rundunar ‘yan sandan jihar Ogun. An ceto wanda aka sace ba tare da kuɗin fansa ba kuma an kai shi…

Read More

Firaminista K.P Sharma Oli na Nepal ya yi murabus yau Litinin bayan matsin lamba daga matasan da suka shafe kwanaki suna jagorantar zanga-zangar adawa da matakinsa na kulle shafukan sada zumunta da suka ƙunshi Facebook da X da kuma YouTube. Da safiyar yau Firaministan ya sanar da murabus ɗinsa, bayan da masu zanga-zangar suka tayar da hatta maganar rashawa da suka ce ta dabaibaye gwamnatin ƙasar ta yankin Himalaya. Masu zanga-zangar waɗanda suka kai ruwa rana tsakaninsu da jami’an tsaro, har ya kai ga kisan mutane 17 bayan da ƴansanda a Kathmandu suka buɗe wuta kan masu zanga-zangar jiya Litinin…

Read More