Nan gaba Tinubu zai iya ciwo bashi daga Opay- Dino Melaye Fitaccen ɗan siyasar Najeriya kuma tsohon Sanata da ya nemi kujerar Gwamnan jihar Kogi Dino Melayi ya yi kakkausar suka ga matakan gwamnatin ƙasar na ciwo bashi babu gaira babu dalili, yana mai cewa yanayin cin bashin da gwamnatin Bola Tinubu ke yi akwai yiwuwar a nan gaba da iya fara ciyo bashi da ƙananun cibiyoyin kuɗi da suka ƙunshi Opay da Moniepoint da sauransu. Sanata Dino Melaye da ke wannan batu yayin zantawarsa da Arise TV jiya Litinin, ya gwada misali da yadda basukan ke ƙoƙarin yiwa Najeriyar…
Author: EDITOR
NLC ta fusata da matakin Najeriya na ƙara albashin masu riƙe da muƙaman siyasa da kashi 114 Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya ta bayyana ɓacin ranta kan matakin gwamnatin Najeriya na ƙara albashin masu riƙe da muƙaman siyasa da kashi 114 cikin 100, wanda ke zuwa a dai dai lokacin da ɗimbin ma’aikata a sassa daban-daban ke kokawa da rashin kyawun albashi. Shugaban ƙungiyar ƙwadagon ta NLC Joe Ajaero a wata sanarwa mai ɗauke dasa hannunshi ya bayyana cewa abin takaici ne matakin ƙara albashin da alawus alawus ga masu riƙe da muƙaman na siyasa dai dai lokacin da galibin ma’aikata…
A ranar Lahadi da daddare, 7 ga Satumba, 2025, wasu ƴan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne sun sace matar da ƴar shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a yankin Patigi na jihar Kwara, Alhaji Muhammad Swasun. Matar, Hajiya Fatima, da ƴar tata, Amina, an ji cewa an sace su ne a garin Sakpefu a yankin Lade na yankin Patigi, inda ƴan bindigar, wanda ake zargin su a matsayin ’yan fashi susu biyar, suka kutsa cikin gidan shugaban ta hanyar tsallake katanga, suna harbi don tsoratar da mazauna wurin. Sun shiga ɗaya daga cikin ɗakunan gidan inda suka samu…
Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa a Abuja fadar gwamnatin Najeriya ta tsunduma yajin aikin gargaɗi na kwanaki 7, da nufin tilastawa gwamnatin ƙasar aiwatar da wasu gyare-gyare a asibitocin birnin. Wata sanarwa da shugaban ƙungiyar George Ebong ya sanyawa hannu ta ruwaito mambobi da sauran manyan shugabannin ƙungiyar na kokawa da halin da asibitoci ke ciki a Abuja, na rashin kayakin aiki da sauran tarin matsaloli. Ko a watan jiya sai da likitocin na Abuja suka roƙi gwamnatin Najeriya ta samar da gyare-gyare a harkokin kiwon lafiyar birnin lura da manyan ƙalubalen da yake fuskanta. Sanarwar ta ruwaito Ebong na…
A Najeriya, an fara wata sabuwar dambarwa tsakanin ƙungiyar direbobin dakon mai da iskar gaz ta NUPENG da matatar Ɗangote, bayan da Attajirin na Afrika ya sanar da sayo motoci dubu 4 da zai yi amfani da su don rarraba man fetur a sassan ƙasar. Wannan mataki na Ɗangote a cewar bayanai na da nufin sauƙaƙa koken jama’a na rashin samun man akan lokaci da kuma tarnaƙin da a wasu lokuta ake fuskanta daga ita wannan ƙungiya ta NUPENG wadda ita ke da alhakin rarraba albarkatun. Sai dai yayinda NUPENG ke cewa magoya bayanta ne ke da hurumin raba mai…
Mahukuntan Isra’ila sun tabbatar da kisan mutane 6 a wani hari da aka kai gabashin birnin Jerusalem yau Litinin, harin da ake alaƙantawa da matsin lambar sojoji da Yahudawan kama wuri zauna a yammacin gaɓar kogin Jordan. Jami’an lafiya a Isra’ila sun ce mutane 12 ne suka jikkata a harin ciki har da wasu 6 da ke cikin mawuyacin hali, sai kuma wasu da dama da rauninsu bai yi girman da za a kaisu ga asibiti ba. Tuni gwamnatin Isra’ila ta bayyana harin a matsayin na ta’addanci, kodayake babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai shi. Da sanyi safiyar…
Iyaye na kokawa da rashin kuɗi dai dai lokacin da makarantu ke komawa sabon zangon karatu. Ɗimbin ɗalibai ne suka koma makarantu yau Litinin a sassan Najeriya kama daga makarantu mallakin gwamnati da kuma masu zaman kansu a sassan ƙasar ta yammacin Afrika mai fama da tarin matsalolin tattalin arziƙi da tsadar rayuwa da ta yiwa jama’arta katutu. A wannan karon an koma makarantun a wani yanayi da farashin kayakin karatu ya sake yin tashin gwauron zabi kama daga shi kansa kuɗin makarantar da littattafan karatu dana rubutu wanda ya sanya iyaye da dama gaza wadata ƴaƴansu da abubuwan buƙata…
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ki amincewa da cewa tsohon gwamna Nasir El-Rufai shi ne jagoransa a siyasance, a maimakon haka ya lissafa Shugaba Bola Tinubu da kuma marigayi lauya mai kare hakkin bil adama Chief Gani Fawehinmi a matsayin manyan masu tasiri a kansa. A cikin shirin TVC na *Politics on Sunday*, Gwamnan ya jaddada yadda yake mai da hankali kan samar da shugabanci mai kyau a Kaduna kuma ya ki amsa Nasir El-Rufai a matsayin mai gidan sa a siyasance. Kuma ya ƙara da cewa dangantakarsa da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta ɗade tun shekarar 1994…
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta kai ɗauki kan waɗanda ambaliyar ta shafa a wasu garuruwan jihar Kaduna, inda ta samu nasarar ceto wasu waɗanda ambaliyar ta rutsa da su. Hukumomi a Isra’ila sun ce wani jirgi maras matuƙi da aka aika daga Yemen ya kai hari kan filin jirgin sama na Ramon Airport a kudancin ƙasar. Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar mutane bakwai a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kauyen Magajin-Wando da ke karamar hukumar Dandume. Firaministan ƙasar Japan Shigeru Ishiba ya yanke shawarar yin murabus a yau lahadi, inda ‘yan…
Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno ya tabbatar da sabon kisan da ‘yan Boko Haram suka yi, inda ya ce mutane 63 ne suka rasa rayukansu. A ranar Asabar, Zulum ya ziyarci al’ummar Darajamal a karamar hukumar Bama don ta’aziyya ga iyalan wadanda aka kashe a daren Juma’a. Wadanda aka kashe sun hada da sojoji biyar da kuma fararen hula kusan 58. Zulum, ya tabbatar da cewa lamarin abun takaici ne kuma abun baƙinciki, ya gana da shugabannin al’ummar wurin kuma ya jajanta wa ga iyalan da suka rasa rayukansu. A cewarsa ga manema labarai, “Muna nan don ta’aziyya…