Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar LP party ya babban tsokaci kan maganar da Dauda Lawan yayi akan jami’an tsaro inda ya bayyana hakan a shafin sa na X. Yana mai cewa, “na karanta koken gwamnan jihar zamfara Dauda Lawal, ya bayyana cewa zai nuna duk inda yan bindiga suke a cikin daji amma kuma jami’an tsaro suna ansan umarnin ne daga Abuja kawai wanda kuma hakan na iya sa yan’ƙasa su cire yardar su akan shugaban ci” Ya ƙara da cewa “rashin iko ga hukumomin tsaro na jihar na ƙara dagula lamarin tsaro a faɗin ƙasar tare da…
Author: EDITOR
Abdulmuminu Jibrin kofa Dan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru/Bebeji a majalisar wakilai ya sanar da ficewa daga jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano, inda ya amince da matakin korar sa da shugaban jam’iyyar ya sanar. Dan Majalisar ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar, inda a ciki ya bayyana cewa bai cancanci kora daga jam’iyyar ba, ba tare an ba shi damar kare kansa ba. Tun da farko, jam’iyyar ce ta sanar da cewa ta kore shi bisa zarginsa da karya dokokinta. Inda ya faɗi cewa, “na yi mamakin ganin an kore ni daga NNPP. Na…
Hukumar kula da aikin Hajji ta ƙasa (NAHCON) ta sanar dasabbin sauye-sauye a cikin tsarin gudanarwarta, bayankammala zama na 14 da ta gudanar daga ranar 26 zuwa 27 ga watan Agusta, 2025. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Hulɗa da Jama’a, Fatima Sanda Usara, ta fitar a ranar Juma’a. A cewar hukumar, sauye-sauyen sun haɗa da mayar da ma’aikatan da aka aro daga wasu ma’aikatu zuwa inda aka samo su a asali, domin rage yawan ma’aikatan da ke gararamba da kuma sake fasalin tsarin aiki. Takardun komawar ma’aikatan an raba su ne a ranar Alhamis, 4…
Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya ce bai kamata wasubambance-bambancen da ke tsakanin ƙasarsa da Amurka su janyo rikicin soji ba. Shugaban ya yi wannan jawabin ne jiya Juma’a yayin daAmurka ta aike da ƙarin jiragen yaƙi 10 zuwa Puerto Rico a kansojojin da aka jibge a ƙasar. BBC ta rawaito Shugaba Maduro baya jin daɗin abin dashugaban Amurka ke yi wa ƙasarsa, kuma hakan ne ya sa ajiya ya ce yanzu kasarsa a shirye take ta tattauna kanabubuwan da Amurka ke buƙata. Gwamnatin Trump ta ce tana murƙushe ƙungiyoyin ‘yandaba dake ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, waɗanda ya ce suna aika…
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da addu’a ga Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa yana da kyakkyawar manufa ga ƙasa da ‘yan ƙasar. Wike ya bayyana hakan a ranar Juma’a a lokacin ƙaddamar da aikin gina hanyar Arterial Road N5 mai lamba 6, wadda ake kira Obafemi Awolowo Way, a Life Camp, Abuja. Ya ce Shugaba Tinubu yana kokarin dawo da karkashin sa a wajen mutanen da suka rasa shi ta hanyar shirinsa na “Renewed Hope Agenda.” Wike ya jaddada cewa dukkan ayyukan da ake ci gaba da yi a…
Wata Ƙungiya daga arewacin Najeriya da Majalisar Matasan Arewa sun gargaɗi gwamnatin tarayya kan kafa ‘yan sandan jihohi a faɗin ƙasar, suna gargadin cewa hakan na iya kara dagula tsaro kuma za a iya amfani da su wajen siyasa. Suna jan hankalin gwamnatin da cewa gwamnoni za su iya amfani da ‘yan sandan jihar wajen kai hari ga abokan hamayyar siyasa, musamman a gab da zaben 2027, saboda an sha ganin yadda ake amfani da ‘yan bangar siyasa a wasu jihohin. Kungiyoyin sun ba da shawarar karfafa hukumomin tsaro na tarayya da ake da su, kamar ‘yan sandan Najeriya, ta hanyar…
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta gayyaci tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai, tare da wasu manyan membobin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), bisa zargin haifar da tashin hankali a cikin al’umma. A cewar wata takarda da aka gani, wadda ya sanya wa hannu Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda mai kula da Sashen Binciken Laifuka (CID), Uzainu Abdullahi, an umurci shugaban ADC na jihar Kaduna da ya gabatar da El-Rufai da wasu mutane a Sashen Binciken Laifuka na Jihar (SCID) a ranar 8 ga Satumba, shekarar da muke ciki. Waɗanda aka gayyata sun haɗa da Bashir Sa’idu, Jafaru Sani, Ubaidullah Mohammed…
Tsaro: Matasa a jihar Sokoto sun sha alwashin kare kansu saboda “sakacin gwamnati” Matasa a karkashin kungiyar Shagari Youths a karamar hukumar Shagari ta jihar Sokoto sun yi barazanar daukar matakin kare kansu sakamakon tabarbarewar tsaro a yankin. Matasan sun kuma zargi gwamnati da sakaci duk da hare-haren ’yan bindiga da ake ta fama da su tare da korafe-korafen jama’a. A cikin wata sanarwa da aka fitar a madadin kungiyar ta hannun Bello Bala Shagari, ya bayyana cewa matasan sun yanke wannan shawara ne a wani taro na yanar gizo da suka gudanar ranar Laraba. Ya ce: “Da dama sun…
Wani taron tsaro da aka shirya a Katsina ƙarƙashin Katsina Security Community Initiative ya rikide zuwa tarzoma bayan wasu ‘yan daba da ake zargin masu goyon bayan siyasa ne suka tarwatsa shi. Taron, wanda ya haɗa kwararru daga bangarorin tsaro, tsoffin jami’an soji da ’yan sanda, masana da shugabannin al’umma, an shirya shi ne domin tattauna hanyoyin magance matsalar tsaro da ta addabi jihar. Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa rikicin ya fara ne lokacin da mai shirya taron, Dr. Bashir Kurfi, yake bayyana matsalolin tsaro a jihar, inda wani ya katse shi da zargin cewa yana sukar gwamnati. Sai…
Ɗan majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin, ya bayyana cewa tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, bai rufe kofar shiga jam’iyyar APC ba gabanin zaɓen 2027. Jibrin, jigo a jam’iyyar NNPP, ya ce Kwankwaso har yanzu ya bar kofar tattaunawa a bude da Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC, duk da kasancewarsa ɗan takarar shugaban kasa a zaɓen 2023. Ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels inda ya ƙara da cewa ƙungiyar Kwankwasiyya ƙarfin siyasa ce da ba za a iya watsi da ita ba. Sai dai ya nuna yiwuwar wasu masu ruwa da tsaki…