Tinubu ya kawar da matsalar rashin biyan albashi a jihohi 27 — Mohammed Idri Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa sauye-sauyen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar sun kawo ƙarshen matsalar biyan albashi a jihohi 27. Ya yi wannan bayani ne a Abuja yayin da kwamishinonin yaɗa labarai daga jihohi 36 suka kai masa ziyara. Idris ya ce manufofin shugaban suna tafiya ne don amfanin ƙasa baki ɗaya, ba siyasa ba, tare da tabbatar da cewa ayyuka suna gudana a dukkan jihohi ba tare da nuna bambanci ba. Ministan ya ce cire tallafin man fetur ya buɗe…
Author: EDITOR
Shugaban kasa Bola Tinubu ya tafi kasashe turai domin gudanar da hutun kwanaki 10, wanda zai fara daga yau Alhamis. Sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar ta ce Tinubu zai shafe kwanakin ne a ƙasashen Turai irin su Faransa da Birtaniya, a wani bangare na hutunsa na aiki na shekarar 2025.
Ƴansanda sun gayyaci shugabar ƙaramar hukumar Tudunwada bisa zargin sanya dogaran ta su harbi wasu ma’aikata Rundunar Ƴansandan Jihar Kano ta gayyaci shugabar karamar hukumar Tudunwada, Sa’adatu Salisu, bisa zargin jagorantar ’yan daba wajen kai hari kan ma’aikatan wata masana’anta a yankin. Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa ma’aikatan masana’antar mai suna Tasarrufi General Enterprise sun kai korafi zuwa rundunar ƴansanda da ke Bompai, inda suka zargi shugabar karamar hukumar, wadda kuma ita ce shugabar Kungiyar Kananan Hukumomi ta Ƙasa (ALGON) , reshen jihar Kano, da umartar ’yan daba da su kai musu hari da adduna tare da bada umarni…