Author: EDITOR

Rundunar ‘yan sanda shiyya ta daya dake nan Kano ta tsare fitaccen ɗan jaridar nan, Ibrahim Ishaq Dan’uwa Rano, bayan wani ƙorafi da daraktan al’amuran gidan gwamnatin Kano Abdullahi Rogo ya shigar, yana zargin ɗan jaridar da bata suna. Rogo dai yana fuskantar bincike daga hukumar EFCC da ICPC kan zargin almundahana da suka kai Naira biliyan 6.5. Jaridar Daily Nigeria ta ce an cafke ɗan jaridar ne a ofishinsa dake nan Kano ba tare da an nuna masa takardar kamu ba, sannan aka wuce da shi kai tsaye zuwa hedikwatar ‘yan sanda ta shiyyar domin amsa tambayoyi. Majiyoyin Jaridar…

Read More

Majalisar dattawan kasar nan ta bayyana damuwa kan gazawar gwamnatin tarayya wajen cika yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar malaman jami’o’i ASUU, inda ta bayyana lamarin a matsayin abin da ba za a amince da shi ba. Shugaban kwamitin majalisar mai kula da manyan makarantu Sanata Aliyu Dandutse, ne ya bayyana hakan bayan zaman sirri da shugabannin ASUU. Wannan na zuwa ne bayan da aka fara yajin aikin gargadi na mako biyu da ASUU ta shiga sakamakon matsalolin da suka dade suna tasowa tun daga shekarar 2011. Ya ce majalisar dattawa za ta fara tattaunawa da dukkan nmasu ruwa da…

Read More

Hedikwatar Tsaro ta kawar da zargin yunkurin juyin mulki a kan Shugaba Tinubu, inda ta bayyana cewa rahotannin gaba daya ba su da tushe, kuma an yi su ne don haifar da damuwa da rashin amincewa a cikin al’umma. A cikin sanarwar da Birgediya Janar Tukur Gusau, Daraktan Bayanai na Tsaro ya fitar, an sanar da cewa soke bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kai na cika shekara 65 shine don ba wa Shugaban Kasa damar halartar wani muhimmin taro na kasashen biyu a waje da kuma ba wa jami’an soji damar ci gaba da mai da hankali kan yaki da…

Read More

Kungiyar magoya bayan Kano Pillars taki amincewa da hukuncin da hukumar shirya gasar gasar Premier ta kasa dauka, bayan hargitsin da aka samu a wasan Kano Pillars da Shooting Stars A wata tattaunawa ta musamman da jaridar Solacebase, shugaban kungiyar magoya bayan Kano Pillars Rabi’u Abdullahi, ya ce basu gamsu da hukuncin ba, domin an yi musu rashin adalci. Ya kara da cewa yanke hukuncin cikin kasa da awa 48 ya nuna cewa akwai wata boyayyar manufa akan Kano Pillars. Abdullahi ya ƙara da cewa ana tuhumar kungiyar da abubuwa guda 9 inda yace wannan ba gaskiya bane, abunda da…

Read More

Hukumomi a Kamaru sun haramta duk wata zanga-zanga a kan titunan babban birnin kasuwancin ƙasar har sai an rantsar da sabon shugaban ƙasar. Matakin ya zo ne bayan wasu manyan zanga-zanga da suka ɓarke a birnin mai tashar jiragen ruwa da kuma a wasu yankunan kasar kan zargin kokrain murde sakamakon zaben da shugaban ‘yan adawa ya tasamma nasara. Tun bayan zaben aka samu hargitsi a lardi na biyar na Douala inda cincirindon mutane suka taru a wajen ofisoshin hukumar zaɓe ta ElCAM sanadin zarge-zargen cusa ƙuri’u a akwatunan zaɓe. Rahotanni sun ce, mazaunan yankin da yawa ne suka taru…

Read More

Gwamnatin Kano ta sanar da kwace gidajen da ba a kammala aikin su ba a rukunin gidaje na Amana da Kwankwasiyya biyo bayan cikar wa’adin da ta bayar. Kwamishinan Ma’aikatar Kula da Gidaje, Arc. Ibrahim Adamu ne ya sanar da haka yayin taron manema labarai a karshen mako. “Biyo bayan yunkuri gwamnati na samar da kyakyawan yanayi wannan guri, gine gine da aka ci kaso mai yawa wajen ginasu, gwamnati ta kara musu wa’adi zuwa karshen watan Disamba domin kammala su”. In ji shi. Kwamishinan ya kuma ce, za su rushe dukkanin gine gine da suka saba da ka’idar biranen…

Read More

Yafiyar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Maryam Sanda tare da karin mutane 174 tana sama tana dabo. A makon da ya gabata ne, shugaban ya yiwa mutane 175 da suka haɗa da ‘yansiyasa, dilolin ƙwaya, da kuma waɗanda suka aikata kisan kai afuwa yayin taron Majalisar Ƙolin ƙasar da ya gudana. Saidai kwatsam akaji wata sanarwa a ranar Alhamis daga ofishin ministan shari’a Lateef Fagbemi wanda shine ya jagoranci kwamitin afuwar, yana mai cewa afuwar da shugaban ƙasa yayi, sai an sake nazari akan lamarin sakamakon ƙorafe-ƙorafen mutane da suke yi. Ofishin ministan ya ƙara da…

Read More

Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ya ce, jam’iyyar APC za ta mamaye jihohi 30 cikin 36 da ke ƙasar nan kafin shekarar 2026. Mohammed ya bayyana haka ne a taron dabarun aiki na watanni uku-uku na shekarar 2025 na ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC wanda aka gudanar a Maidugurin jihar Borno. Taron ya mayar da hankali kan yadda za a inganta haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohin da APC ke mulki. Ministan kuma ya ce, yawaitar sauya sheka zuwa APC na faruwa ne saboda kyawawan manufofi da shirye-shiryen shugaba Tinubu. Ya kuma ce, hakan ya haifar da ingantaccen mulki da…

Read More

Ma’aikatar ilimi ta bayyana cewa daga yanzu ba dole ba ne sai ɗaliban da ba su da alaƙa da kimiyya da fasaha sun ci darasin lissafi a jarabawarsu ta kammala sakandire kafin samun gurbin karatu a manyan makarantun ƙasar. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da daraktar yaɗa labaran ma’aikatar ilimin tarayyar Najeiyar, Folasade Boriowo, ta sanya wa hannu a Talata, inda take cewa gwamnatin ƙasar ce ta amince da sabon tsarin gyaran sharuɗan karɓar ɗalibai a dukkan manyan makarantun ƙasar, domin sauƙaƙa samun damar shiga jami’a da sauran cibiyoyin ilimi. Sanarwar ta bayyana cewa wannan mataki ya shafi…

Read More

Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah reshen jihar Kaduna ta bukaci gwamnatin jihar ta gaggauta biyan diyya ga iyalan Fulani da suka rasa ‘yan uwansu a harin da aka kai musu a kauyen Tanda, da ke Karamar Hukumar Jema’a dake Kudancin Jihar Kaduna. Shugaban kungiyar, Abdulhamid Musa Albarka, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce, harin da aka kai ranar 28 ga Watan Satumba ya nuna yadda manoman yankin ke cin karensu ba babbaka akan Fulani makiyaya. “Harin ya yi sanadiyyar rasuwar Suleiman Idris, yayin da wasu makiyaya 6 suka samu munanan raunuka, bayan da…

Read More