Wata sabuwar ƙungiyar ƴanta’adda da ake kira Wulowulo ta ɓulla a ƴankin arewa ta tsakiyar Najeriya, a dai-dai lokacin da ƙasar ke fama da ɗimbin matsalolin tsaro. Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya bayyana haka yayin gudanar da wani babban taron masu ruwa da tsaki a Lafia, ya kuma danganta sabuwar ƙungiyar da ‘yan Boko Haram. Sule ya ce wasu daga cikin ‘ƴa’ƴan ƙungiyar na kai hare-hare a jihar Kwara da wasu ƴankunan dake arewa ta tsakiya. Gwamnan ya kuma nemi haɗin kan jami’an tsaro domin daƙile ayyukan ƴanta’addan waɗanda suke bazuwa a jihohin dake yankin. Sule ya ce ganin…
Author: EDITOR
Majalisar Wakilai ta ƙaddamar da bincike kan ƙaruwar koke-koken ’yan kasa kan yawan cire musu kuɗaɗe ba tare da bayani ba daga asusun ajiyarsu da bankunan kasuwanci ke yi. Wannan mataki ya biyo bayan amincewa da wani ƙuduri da ɗan majalisa Tolani Shagaya daga jihar Kwara ya gabatar, inda ya nuna damuwa kan abin da ya kira, cire kuɗaɗe ba tare da bayani ba, da kuma yawan kuɗaɗen da ake karɓa ba bisa ka’ida ba, duk da dokokin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kafa. Yayin gabatar da ƙudurin a zaman majalisa ranar Talata, Shagaya ya duk da cewa ana…
Guda cikin ƴan takarar neman kujerar shugabancin ƙasar Kamaru ya yi ikirarin lashe zaɓen ƙasar Issa Tchiroma Bakary wanda ke kan gaba a bayanan alkaluman zabe na bayan fage ya yi ikirarin lashe zaɓen ƙasar inda ya yi kira ga shugaba mai ci Paul Biya da ya amsa shan kaye tare da girmama zaɓin jama’ar ƙasar. Dan takarar daga jam’iyyar adawa ya bayyana hakan ne a wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, a tsakar daren Litinin. Mista Bakary ya gode wa al’ummar Kamaru kan ”yarda da samar da canji” da ya ce sun yi a ƙasar.…
Iyalan Marigayi Bilyaminu Bello wanda matarsa Maryam Sanda ta hallaka kuma kotun Koli ta tabbatar hukuncin kisa a kanta sun yi martani ga afuwar da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi mata. Dakta Bello Muhammad ya kalubalanaci afuwar da kuma sakinta a cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin iyalan marigayin a ranar Litinin. “Bai kamata shugaba Tinubu ya hada da Maryam Sanda cikin masu laifin da ya yiwa afuwa ba, saboda hakan tamkar fami ne kan raunin da muka fara warkewa daga gare shi. “Yin wannan afuwa ga Maryam Sanda rashi adalci ne garemu.” In ji sanarwar. Dangin…
Ma’aikatar Shari’a da haɗin gwiwar Hukumar Wayar Da Kai Ta Ƙasa (NOA) sun ƙaddamar da gagamin wayar da kan jama’a kan laifukan da ake aikatawa a intanet (cybercrime) a faɗin ƙasar nan. An kaddamar da gangamin ne na Cybercrime Awareness Walk na 2025 a Babban Birnin Tarayya Abuja, a ranar Litinin. Hukumomin biyu sun buƙaci jama’a, musamman matasa da su kasance masu lura da amfani da fasahar zamani cikin gaskiya da aminci. Barista Tessy Nnalue da ta wakilci Daraktan Hukumar NOA, ta tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da gangamin a rediyo, da talabijin, da fassara shi a…
Majalisar ƙasa ta gabatar da sabon shirin da ke neman sauya lokacin zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnoni na 2027 zuwa watan Nuwamba 2026, maimakon watan Fabrairu ko Maris kamar yadda aka saba. Wannan mataki yana cikin gyaran dokar zaɓe ta 2022, wanda ya tanadin cewa za a iya gudanar da zaɓe kafin kwanaki 185 da ƙarewar wa’adin gwamnati mai ci, wanda ke ƙarewa a ranar 29 ga Mayu. Manufar shirin shine, samar da isasshen lokaci don kammala dukkan ƙorafe-ƙorafen dake gaban kotunan zaɓe kafin rantsar da sabbin shugabanni. A yayin taron jin ra’ayoyi da kuma kwamitin haɗin gwiwa na…
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wasu matasa biyu da suka nutse yayin wanka a rafin da ke Hayin Yawa Gada, ƙaramar hukumar Tudun Wada ta jihar. Mai magana da yawun hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na rana a ranar Alhamis, 9 ga Oktoba, 2025. Ya ce ofishin hukumar da ke Tudun Wada ya samu kiran gaggawa daga jami’in Hisbah wanda ya sanar da cewa matasan da suka nutse sun kasance Habu Sani da Haruna Isah, dukkansu masu shekaru kusan 15. Jami’an hukumar sun miƙa…
Wani Likitan ƙwaƙwalwa a Asibitin Neuropsychiatric Aro, a Abeokuta, Jihar Ogun, Dokta Emmanuel Abayomi ya ce kimanin mutane miliyan 60 ne ke fama da taɓin hankali a halin yanzu. Ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma’a a Abeokuta a wajen wani taron ƙarawa juna sani da Ƙungiyar likitocin ƙwaƙwalwa ƙarƙashin Ƙungiyar masu ruwa da tsaki ta ƙasa ta shirya domin tunawa da ranar kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa ta duniya ta bana. Shirin da Ash Montana Deck tare da haɗin gwiwar Atlantis, Americana 1 da Longhorn Deck suka yi wanda ya ja hankalin ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a jihar.…
’Yan Sandan sun samu nasarar ceto wasu mutum uku da aka sace, bayan wani samame da ta kai a jihohin Kano da Kaduna. A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya bayyana cewa an gudanar da samamen ne tsakanin ranar 7 zuwa 9 ga watan Oktoba, 2025, bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori. A cewar Kiyawa, samamen farko ya gudana ne a ranar 7 ga watan Oktoba. Ya ce runduna ta musamman ta yaƙi da garkuwa da mutane tare da haɗin gwiwar tawagar sintiri ta sashen ’yan sanda na Bebeji…
Sojojin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun kashe ‘yan ta’addan ISWAP 15 a wani mummunan hari da suka kai a Ngamdu, karamar hukumar Kaga ta jihar Borno. wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar hadin gwiwar Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar ya ce ‘yan ta’addan sun kai harin ne da manyan bindugu samfurin RPG, da jiragen yaki marasa matuki da kuma bama-baman kirar (IEDs) domin kai hari kan sojoji da motocinsu. Saidai duk da tsananin harin, sojojin sun tsaya tsayin daka wajen mayar da martani da karfin wuta, wanda ya jawo mummunar asarar rayuka ga ‘yan ta’addan. sanarwar…