Author: EDITOR

Jami’an agaji na ci gaba da zakulo gawawwakin mutane daga ɓaraguzan gini a Gaza yayin da janyewar dakarun Isra’ila ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki a ranar Juma’a. An kiyasta cewa mutum 200,000 ne suka koma gidajensu a yankin arewaci zuwa yanzu. Da dama sun ce sun kaɗu matuƙa da irin girman ɓarnar da aka yi. Shugaban Amurka Donald Trump ya kara bayar da tabbacin cewa za a mutunta jarjejeniyar, yana mai cewa “dukkaninsu sun gaji da yaƙin, wannan lamari ya sha gaban Gaza, wannan zaman lafiya ne a Gabas ta Tsakiya. Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ce…

Read More

Wani lauya mai suna Johnmary Chukwukasi Jideobi a Abuja ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya a Abuja (ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/2102/2025) don hana tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya, Goodluck Jonathan, tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ko wani zaɓe na gaba. Ƙarar, wadda aka shigar ta sanya Jonathan a matsayin wanda ake ƙara na farko, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) a matsayin ta biyu, da kuma Babban Lauyan Gwamnati (AGF) a matsayin na uku. Jideobi ya ce, Jonathan ya ƙare wa’adin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada a sashi na 137(3). “Mutumin da aka rantsar…

Read More

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta koma aikin ta a matsayin ‘yar majalisar Dattajai bayan karewar wa’adin dakatar da ita da Majalisar ta yi na watannin shida Majalisar ta dakatar da Sanatan mai wakiltar Kogi ta tsakiya a matsayin ladabtarwa na abin da suka kira karya dokarsu a zauren majalisa. Maris 2025. Rahotanni sun ce tun a ranar 23 ga watan Agusta aka ga an buɗe ofishinta na majalisa da aka rufe, amma sai a yau 7 ga wata ta shiga tare da kama aiki yadda ya kamata. A ranar 20 ga watan Fabrairu shekarar 2025 aka fara samun takun saƙa tsakanin…

Read More

Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa Jihar Filato Alama ce ta Jajircewa ga Haɗin Kan Ƙasa, a cewar Gwamna Mutfwang A ranar 4 ga Oktoba, 2025, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci ga, babban Jihar Filato, don halartar jana’izar Lydia Yilwatda Goshwe, mahaifiyar Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda. Taron, wanda aka gudanar a Cocin Christ in Nations (COCIN), ya jawo hankalin fitattun mutane ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da gwamnoni daga Ƙungiyar Gwamnonin APC. Kalaman Gwamna Mutfwang Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato, wanda memba ne na jam’iyyar adawa ta PDP, ya yaba wa ziyarar shugaban…

Read More

Shugaban kungiyar iyayen yaran Kano da aka sace Kwamared Isma’ila Ibrahim Muhammad ya sanar da da cewa sun sake gano yara 8 ‘yan asalin jihar Kano da aka sace a jihar Delta. Wannan na zuwa ne daidadi lokacin da ake ci gaba da fadada bincike kan batan sama da yara 100, a cikin shekaru 5 da suka wuce. Da yake ganawa da manema labarai Shugaban kungiyar Kwamared Isma’ila Ibrahim Muhammad, ya yi ki ga iyayen yaran da su ziyarci hukumar NAPTIP domin tanatacewa ko da Yaransu a cikin 8 din da aka gano a yanzu. Kwamared Isma’ila Ibrahim Muhammad, ya…

Read More

Matasa shida daga Najeriya ne suka samu nasarar lashe gasar Hadisi da Gidauniyar Sarkin Moroko Mohammed na shida ta shiryawa Malaman Afrika. Ɗaya daga cikin alkalan gasar, Dr. AbdulGaniyu Tijani, ne ya bayyana hakan yayin bikin rufe gasar da aka gudanar a birnin Abuja a ranar Asabar. Ya ce waɗanda suka lashe kyautar a rukuni na farko su ne Fatima Turbo, Muhammad Ibrahim, da Abubakar Abba, dukkansu daga jihar Borno. A rukuni na biyu kuwa, akwai Saleh Al-Amin daga Borno, Ahmed Kolawole daga Kwara, da Khalifah Jibril daga Kaduna sune suka fito zakaru. Kowane rukuni mutane uku ne suka yi…

Read More

Shugaban sashen ilimin Ƙasa (Geography) na Jami’ar Northwest da ke Jihar Kano, Dakta Nazifi Umar Alaramma ya yi kira ga gwamnatin taraiya da ta sanya darasin ‘ Geography’ ya zama wajibi ga daliban sakandare a cikin manhajar karatu ta ƙasa saboda muhimmacinsa. DAILY NIGERIAN HAUSA ta tuna cewa a shekarar 2013 ne gwannatin tarayya ta cire darasin ilimin Geography a matsayin dole ga ɗaliban sakandare Inda ya koma a matsayin zabi. Saidai kuma Alaramma, a taron manema labarai gabanin Babban Taron Kungiyar Masana Ilimin Ƙasa ta Najeriya (Association of Nigerian Geographers, ANG) da jami’ar Northwest za ta karbi bakuncinsa na…

Read More

Mutuwar shugaban mata (women leaders) Biyar a Karamar Hukumomin Lagos Ya Haifar da Bincike kan zargin ƙungiyar asiri A cikin wani labarai gidan jaridar Vanguard ta wallafa ta ruwaito cewa mutuwar yan’siyasr har su biyar Karamar Hukumomi na Jihar Lagos, ya bar baya da ƙura mutuwar ta matan waɗanda masu rinjaye a cikin al’umma ba zato ba tsammani kuma ƙasa da wata biyu ya sa mutane da hukumomin yankin suka koma neman taimako daga al’ada, malaman coci da limamai. Lamarin, wanda aka ruwaito a wasu Karamar Hukumomi kamar Somolu, Bariga, da wasu a yankunan mainland da Ikorodu, ya haifar da…

Read More

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sunkai hari gidan Dr. Ifeanyi Ogbu, sanannen likitan dabbobi kuma tsohon shugaban kungiyar likitocin dabbobi ta Najeriya (NVMA) a yankin A birnin tarayya, a gundumar Kubwa da ke hanyar Kubwa-Kaduna a Abuja. Maharan sun harbe Dr. Ogbu inda nan take ya mutu a lokacin harin, sannan suka sace yaransa uku, wadanda har yanzu ba a gano inda suke ba. Dr. Ifeanyi Ogbu, wanda abokan aikinsa suka bayyana a matsayin kwararre a fannin likitan dabbobi ne a Abuja. Daren Juma’a, 3 ga watan Oktoba, aka ga gawarsa,Dr. Ogbu ya mutu bayan an…

Read More

Majalisar dokokin Chadi ta amince da shirin yiwa kundin tsarin mulkin ƙasar garambawul wanda zai bai wa shugaban ƙasa Mahamat Idriss Deby damar ci gaba da takarar zabe ba tare da adadi ba. Yan majalisu 236 suka goyi bayan shirin, yayin da guda yaki amincewa da shi daga cikin ƴan majalisu 257 dake majalisar dokokin. Mahamat ya zama shugaban ƙasa na rikon kwarya a shekarar 2021 sakamakon rasuwar mahaifinsa Idris Deby wanda ya kwashe shekaru 30 yana mulkar Chadi. Mahamat ya ɗauki alkawarin gudanar da shugabancin rikon kwarya na watanni 18, amma kuma sai ya tsawaita shi zuwa shekaru biyu.…

Read More