Karamar Hukumar Karaye ta kaddamar da shirin dasa bishiyu iri daban-daban ga al’ummar yankin. Babban Daraktan Kudi da Gudanarwa na Karamar Hukumar Karaye, Alhaji Abdu Mahmuda Doguwa, ya jagoranci bikin a madadin shugaban karamar hukumar, Alhaji Haruna Safiyanu Karaye. Ya kuma yi karin haske kan muhimmancin bishiyu wajen rage kwararowar Hamada da kuma samar da tsaftataccen muhalli. A nasa jawabin, shugaban sashin noma da albarkatun kasa na Karamar Hukumar Karaye, Malam Mai Kudi Abdu Kiru, ya bayyana cewa gwamnati ta raba bishiyu dubu goma (10,000) ga al’umma, wadanda suka hada da Darbejiya, Rimi, Madaci, Dogon yaro, Dorawa, da sauran su.…
Author: EDITOR
Hukumar jin dadin alhazai ta Kano ta tabbatar da cewa ranar 8 ga Oktoba, 2025 ne ƙarshe wa’adin biyan kashi 50% na kujerun Hajjin bana. Shugaban Hukumar Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar Alhamis a ofishinsa. A cewarsa, hukumar Kula Da Alhazai ta Kasa (NAHCON) ce ta bayar da wannan umarni, inda ta wajabta wa kowace jiha ta tura rabin kujerun da aka ware mata kafin ko a ranar 8 ga Oktoba, 2025. Dambappa ya bukaci masu niyyar zuwa aikin Hajji da su yi gaggawar aiwatar da…
Ɗaya daga cikinsu ta sha alwashin cewa sai ta tabbatar an gurfanar da mahafinta a gaban kotu kan yunƙurin safararta da ya yi zuwa iraƙi, in ji jami’in hukumar NAPTIP. Hukumar da ke yaƙi da safarar mutane ta Nijeriya (NAPTIP) ta ce ta kama aƙalla mutum biyar da ake zargi da safarar mutane tare da kuɓutar da mutum 24 a filin jiragen saman ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe International Airport, da ke Abuja. Jami’in watsa labaran hukumar NAPTIP na ƙasa, Vincent Adekoye, ya bayyan a ranar Laraba cewa a cikin waɗanda aka kama akwai wani mutum da ya yi…
Gwamnatin jihar Kano ta ce za a yada zaman da za yi da Sheikh Lawan Shui’aib Abubakar limamin masallacin Triumph kai tsaye a kafafen yada labarai domin cire shakku daga zukatan al’umma. Sakataren Majalisar Shura Shehu Wada Sagagi ne ya bayyana haka a hirarsa da manema labarai a maraicen ranar Laraba. “Za a fara da aikewa da malamin takardar gayyata wadda kuma za ta ƙunshi rana da lokacin da zai bayyana a gaban kwamitin.” Shehu Sagagi ya kuma ce, ba wai an dakatar da Triumph daga yin wa’azi ba ne kwata-kwata, an dakatar da shi ne daga tattauna batun da…
Kwamishinan ‘Yan Sanda na birnin tarayya Abuja ya bayyana irin kokarin rundunar take yi na tabbatar da tsaro birnin. Hakan ya biyo bayan mutuwar watan Mai Gabatar da Labarai a tashar Talbijin ta Arise TV A ranar 1 ga Oktoba, 2025. ‘Yar jaridar Somtochukwu Christelle Maduagwu da aka fi sani da “Sommie”—‘yar shekara 29, mutuwarta a birnin. ‘Yar jaridar ta gamu da ajalinta ne a lokacin wani fashi da makami a gidanta da ke yankin Katampe a Abuja a ranar 29 ga Satumba, 2025, Hakan ya sa hukumomin tsaro suka dauki mataki cikin gaggawa, a bayanin Kwamishinan ‘Yansandan birnin CP…
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce ƙasar ta samu gagarumin ci gaba tun bayan samun yancin kai a 1960. Yayin wani jawabi da ya gabatar wa ƙasar albarkacin cikar Najeriya shekara 65 da samun yancin kai, Shugaba Tinubu ya ce ƙasar ta samun ɓunkasa a fannin tattalin arziki da ci gaban zamantakewa da fannin ilimi. ”…dole ne a yaba wa ci gaban da ƙasarmu da samu. A yau Najeriya ta samu wadatuwar fannonin ilimi da kiwon lafiya fiye da lokacin da muka samu yancin kai”, in ji shi. Shugaban na Najeriya ya ce a lokacin da ƙasar ta samu yancin…
An dakatar da ayyukan gwamnatin tarayya a Amurka bayan kasa samun jituwa tsakanin ƴanmajalisar Democrats da Republican game da kasafin kuɗin ƙasar. Matakin ya shafi ayyukan yau da kullum, kuma ma’aikata da dama ba za su samu albashi ba. Wannan ne karon farko da aka rufe harakokin gwamnati bayan shekaru bakwai. Gwamnatin za ta ci gaba da zama a rufe har sai ɓangarorin biyu sun cimma matsaya. Ƴan Democrats na neman dawo da kuɗaɗen da aka zabtare na inshorar lafiya. Donald Trump ya yi gargaɗin yin amfani da damar domin korar ma’aikata da kuma rage wasu ayyukan gwamnati
Shugaban hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta Najeriya FIRS Zacch Adedeji ya bayyana cewa kuɗaɗen shigar da suke tattarawa gwamnatin ƙasar ya ƙaru da kashi 411 cikin watannin baya-bayan nan sai dai duk da haka gwamnatin ƙasar za ta ci gaba da ciyo basuka don tafiyar da ayyuka. Da ya ke amsa tambaya game da dalilin ci gaba da ciyo bashin, Mr Adedeji ya musanta cewa cin bashin nada nasaba da gazawar gwamnati, maimakon haka shugaban na hukumar FIRS ya ce basukan da ke kan Najeriyar manuniya ce ta ƙarfin tattalin arziƙi da kuma yadda gwamnati ke baza koma ko kuma…
Aƙalla mutane dubu 62 da 700 aka tabbatar da cewa sun mutu sakamakon cutuka masu alaƙa da tsananin zafi a ƙasashen nahiyar Turai cikin shekarar da ta gabata ta 2024 kamar yadda mujallar lafiya ta Nature Medicine ta wallafa a farkon makon nan. Masu bincike a cibiyar Global Health da ke Barcelona a Spain waɗanda ke bibiyar mace-macen da ake fuskanta sanadiyyar zafin sun ce daga shekarar 2022 zuwa 2024 mutane dubu 181 daga ƙasashe 32 tsananin zafin ya kashe a Turai. Rahoton ya bayyana cewa Mata da Tsofaffi da kuma ƙananan yara su ne kan gaba da yanayin na…
Masana a fannin diflomasiyya na ci gaba da tsokaci game da matakin ƙasashen haɗakar AES da suka ƙunshi Nijar Mali da kuma Burkina Faso na sanar da shirin ficewa daga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC. Kotun ta ICC mai shalkwata a birnin Hague na Netherlands a shekarar 2002 ne aka samar da ita, da nufin saurara tare da aiwatar da hukunci kan manyan laifuka walau tsakanin shugabanni ko jagororin ƙasashe ko kuma abin da ya shafi rikici tsakanin ƙasashe biyu da ya kai ga yaƙi ko babban rikici. Sai dai wata sanarwa da ƙasashen 3 suka fitar game…