Author: EDITOR

Rahoton wani kwamiti da Gwamnatin jihar Filato ta kafa don bincike game da hare-haren da ake kaiwa sassan jihar ya gano cewa maharan sun fito ne daga maƙwabtan jihar da suka ƙunshi Kaduna da Bauchi da kuma Taraba. Kwamitin wanda tun farko gwamna Caleb Mutfwang ya kafa da nufin lalubo hanyoyin magance matsalolin da jihar ke fama da su na hare-hare masu alaƙa da ƙabilanci ko addini, na zuwa ne bayan tsanantar makamantan hare-haren a shekaru 2 da suka gabata. Shugaban kwamitin Manjo Janar Rogers Ibe Nicholas, ya ce bayan tattaunawa da mabanbantan ƙabilu da kuma ziyartar yankunan da hare-haren…

Read More

Mahukuntan jihar Bauchi a Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane 58 sanadiyyar ɓarkewar annobar cutar amai da gudawa ko kuma kwalara da ta shafi ƙananan hukumomin jihar 14 daga cikin 20. Bayanai sun ce baya ga mutanen 58 da cutar ta kashe akwai kuma mutane aƙalla 258 da yanzu haka ke kwance sanadiyyar cutar kuma suke karɓar kulawa don ceto rayuwarsu. Mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Auwal Mohammed Jatau da ke bayyana haka yayin ƙaddamar da wasu kwamitin ƙwararru har guda 2 don tunƙarar wannan annoba, ya ce sake samun ɓarkewar cutar ta tayar da hankalin gwamnati matuƙa. A cewar mataimakin…

Read More

Mamallakan katafariyar kasuwar zamani ta Shoprite sun musanta jita-jitar kulle ilahirin kasuwancinsu da ke sassan Najeriya, wanda ke da alaƙa da durƙushewar wasu daga cikin shagunan tallata kayakinsu. Bayanai na nuna cewa da dama daga cikin shagunan na Shoprite na fama da ƙarancin kayakin saidawa lamarin da ke nuna yiwuwar, jita-jitar ta iya zama gaskiya. Sai dai wata sanarwa da Shoprite ya fitar, ya ce rashin kayakin cinikayyar da ake gani a rassan shi ba ya nufin suna da shirin kulle shagunansu a sassan Najeriya, hasalima za su sake bunƙasa kasuwancin nasu ne. Shoprite wanda ke da ɗimbin masu zuba…

Read More

Jakadan Algeria a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya Amar Bendjama ya nemi afuwar Falasɗinawa bayan da ya ce an kange duk wani yunƙurinsu na kai ɗauki ga halin da suke ciki sakamakon yaƙin kusan shekaru 2 da Isra’ila ke ci gaba da ƙaddamarwa a kansu da zuwa yanzu ya kashe mutanen da yawansu ya tasamma dubu 66. Da ya ke jawabi bayan tashi daga zaman kwamitin sulhu na Majalisar a birnin New York jiya Alhamis, kafar Aljazeera ta ruwaito Bendjama na cewa ‘‘ƴan uwanmu Falasɗinawa Maza da Mata ku yafe mana’’. ‘‘ Ku yafe mana saboda mun gaza, mun gaza isar…

Read More

Na ƙalubalanci Ganduje da ya nuna aiyuka 4 da ya kammala a shekaru 8 na mulkin sa a Kano – Gwamna Abba Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya caccaki tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje, inda ya zarge shi da wawure dukiyar talakawa ba tare da ya yi wani aikin a zo a gani ba. Da ya ke jawabi a yayin rabon takardar daukar aiki na dindindin ga malaman BESDA su 4, 315, wanda ya gudana a filin wasa na indo a jihar Kano a yau Alhamis, gwamna Abba ya ƙalubalanci Ganduje da ya nuna aiyuka hudu kacal da ya…

Read More

Wata fitacciyar mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam da Muhalli a jihar ribas tace Shugaba Tinubu baya jin tausayin mutanen jihar Ribas A cewar Ann-Kio Briggs, shugaban kasa Bola Tinubu bai ji tausayin mutanen jihar Rivers ba game da ɗaga da dokar ta-baci da aka sanya a jihar na tsawon watanni shida. A cewarta, an sanya dokar ta-baci saboda rikicin siyasa tsakanin tsohon gwamna Nyesom Wike da gwamna Siminalayi Fubara, wanda bai shafi jama’ar jihar ba. Briggs ta ƙara da cewa mutanen jihar Ribas sun sha wahala a tsawon watanni shida ba tare da wani amfani ba, saboda hana gwamnati…

Read More

Trump ya shigar da ƙarar jaridar New York Times tare da neman diyyar dala biliyan 15 Shugaba Donald Trump na Amurka, ya nemi diyyar dala biliyan 15 daga kafar yaɗa labarai ta New York Times da wasu ma’aikatanta guda 4 kodayake tuni kafar ta yi watsi da wannan ƙara bayan da ta ce bata cika sharuɗɗan da ya kamata ba. Tun a Litinin ɗin farkon makon ne kotun yanki a birnin Florida ta aike da wannan tuhuma ga New York Times, dangane da wasu dogayen rubutu da kafar ta yi dama wani littafi guda da aka wallafa kuma jaridar ta…

Read More

Amnesty ta bayyana wasu kamfanoni 15 da ke ɗaukar nauyin yaƙin Isra’ila a Gaza Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta fitar da wani rahoto da ke nuna wasu manyan kamfanonin duniya 15 a matsayin waɗanda ke goyon bayan kisan ƙare dangin da Isra’ila ke yi a Gaza. Amnesty International ta ce kamfanonin 15 na taimakawa Isra’ila wajen take haƙƙoƙin ɗan adam tare da keta dokokin ƙasa da ƙasa a kisan ƙare dangin da ƙasar ke ci gaba da aikatawa a Gaza yayin yaƙin kusan shekaru 2 da ta ke da mayaƙan Hamas. Rahoton na Amnesty ya ce…

Read More

Tsohon gwamnan Kano ya yabawa gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf bisa ƙoƙarin sa akan harkokin ilimi a jihar. Hakan ya biyo bayan da aka saki saka makon jarabawar kammala karatun sakandare ‘NECO’ inda aka bayyana ɗaliban jihar Kano ne ke kan gaba wajan samun nasar. Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso ya taya daliban Kano murna bisa samun nasara a jarrabawar kammala sakandare ta kasa (SSCE) da Hukumar NECO ta gudanar a shekarar 2025. Kwankwaso ya ce wannan nasara ba ta zo a banza ba illa sakamakon jajircewar Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Mai Girma Gwamna Alhaji Abba…

Read More

Ministan harkokin wajen Ghana, Samuel Okudzeto Ablakwa, ya bayyana cewa ƙasar za ta karɓi ƙarin mutum 40 da za a kora daga Amurka a kwanaki kaɗan masu zuwa. Bayanin ministan na zuwa ne bayan ‘yan majalisar dokokin Ghana na jam’iyyu marasa rinjaye sun soki matakin gwamnati na karɓar mutum 14 da aka kora daga Amurka ba tare da neman izinin majalisa ba. Ya bayyana cewa Ghana ta ɗauki wannan mataki ne domin jinƙai bayan ta lura da irin mawuyacin halin da ake saka waɗanda da aka kora daga Amurka. “Ba wai mun yarda da wannan shiri ba ne don mun…

Read More