Hukumomin Spain sun yi barazanar cewa da yiwuwa ƴan wasan tawagar ƙasar ba za su halarci gasar kofin duniya ta badi ba, idan har Isra’ila ta samu tikitin shiga gasar. A cewar mai magana da yawun jam’iyyar Socialist Workers mai mulki a ƙasar ta Spain, Patxi Lopez, za su nazarci lamin yadda ya kamata. Wannan dai na daga cikin matakan da Spain ɗin ke ɗauka na nuna rashin goyon bayanta ga hare-haren da Isra’ila ke kaiwa yankin Gaza, wanda a farkon wannan makon Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar da cewa Isra’ilan na aikata kisan ƙare dangi ne ga Falasɗinawa. Rabon…
Author: EDITOR
Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa ta kaddamar da shirin bayar da kulawar lafiyar gaggawa kyauta ga yara a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano dake nan Kano. Shirin, a cewar Darakta a hukumar, Dr. Salahudeen Sikiru, wani bangare ne na fadada shirin lafiyar iyaye da hukumar ke aiwatarwa zuwa ga yara masu rauni da masu bukata ta musamman. Ya ce an fara shirin fiye da shekara ɗaya da ta gabata da nufin rage mace-macen jarirai ’yan kasa da shekaru biyar. Ya kuma ce a karkashin shirin, yara da ke fama da matsalolin gaggawa kamar rashin numfashi, amosanin jini, cutar…
A jiya da misalin da misalin ƙarfe 6 da minti 50 shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya Sauka filin jirgin saman Namadi Azikwe dake Abuja, Shugaban ƙasa Tinubu ya tafi Birtaniya da kuma Faransa a ranar 4 ga watan Satumba a matsayin hutun shekara, sai dai mai magana da yawun shugaban ƙasa a kafar sada zumunta Bayo Onanuga ya sanar da cewa shugaban zai dawo ƙasar. Sai dai a wani ɓangaren ana zaton cewa wa’adin dakatarwar da akayi wa gwamnan jihar ribas ya zo ƙarshe inda ake tunanin shugaban ƙasar zai janye dakatarwar a ranar Alhamis. A ranar 18 ga…
Darajar takardar kuɗi ta Najeriya Naira ta ɗaga a kasuwar musayar kuɗaɗen ƙetare yau Talata, inda ake sayar da kowacce dala guda akan ƙasa da farashin naira dubu 1 da 500. Bayanai sun ce buƙatar tsabar takardar kuɗin ta naira ya sanya saukar farashin dalar wanda ya taimakawa asusun ajiyar kuɗaɗen ƙetare na Najeriyar wanda a ranar 11 ga watan nan ya kai dala biliyan 41 da miliyan 660. Babban bankin Najeriyar CBN ya ce ana sayar da kowacce dala guda kan naira dubu 1 da 498 zuwa dubu 1 da 507, wanda ke nuna gagarumar nasara daga yadda aka…
Majalisar dattijan Chadi na gab da kaɗa ƙuri’a kan wani ƙudiri da ke tsawwaita wa’adin shugabancin ƙasar suwa shekaru bakwai-bakwai saɓanin biyar-biyar da ya ke a kundin tsarin mulkin ƙasar baya ga sahale shugaban ƙasar Mahamat Idris Deby damar neman wa’adi marar adadi. Ƙar ƙashin wani ƙudiri da jam’iyya mai mulki ta MPS ta gabatar da nufin gyara a kundin tsarin mulkin cikin watan Disamban 2023, ya nemi sauya dokar da ke taƙaitawa shugaban damar riƙe muƙamin shugabancin wata ƙungiya ko jam’iyyar siyasa. Tuni Majalisar wakilan Chadi ta aminta da wannan ƙudirin bayan kaɗa ƙuri’a da ya samu amincewa mambobi…
A Najeriyar wasu alƙaluma sun nuna sake samun sauƙin hauhawar farashi da tsadar rayuwa a sassan ƙasar cikin watan da ya gabata na Agusta, kamar yadda hukumar ƙididdiga ta NBS ke cewa a wani rahotonta na wata-wata. A cewar NBS hauhawar farashin ta ragu daga kashi 21.88 a watan yuli zuwa kashi 20.12 a watan Agusta, yayinda kayakin masaraufi ke ci gaba da sauka. Tuni ƴan Najeriya suka fara samun sauƙin hauhawar farashin kayakin amma waɗanda ake samarwa a cikin gida, wanda ke nuna cewa babu sauƙin kan kayakin da ake shigarwa cikin ƙasar da ke ƙetare. An dai fi…
Masana a ɓangaren kiwon lafiya sun koka da yawaitar mace-macen fuju’a ko kuma mutuwar kwaf-ɗaya da ake ganin ta’azzararta a sassan Najeriya, ta yadda mutane kan yanke jiki su mutu nan ta ke ba tare da alamu ko jinyar wata cuta ba. Masanan sun bayyana yawaita mutuwar ta kwaf ɗaya a matsayin babban ƙalubalen lafiya da ke buƙatar ɗaukar matakan gaggawa musamman ta fannin ganin mutane sun rungumi tsarin duba lafiyarsu akai-akai. Duk da cewa babu cikakkun alƙaluman mutanen da ke mutuwar ta kwaf-ɗaya a sassan Najeriya, amma a baya-bayan nan ana ganin yawaitar masu wannan mutuwa ta Fuju’a a…
Wata alƙaliyar kotun Amurka ta soki matakin Donald Trump na tisa ƙeyar ƴanciranin ƙasashen yammacin Afrika da suka ƙunshi ƴan Najeriya da Gambia zuwa Ghana. Alƙaliyar kotun gundumar Washington Tanya Chutkan ta ce akwai hujjoji daga lauyoyin ƴanciranin da ke nuna cewa zasu fuskanci azabtarwa da ko kuma miƙasu gaban kotu matuƙar aka mayar da su ƙasashensu. Hasalima Alƙaliyar ta bayyana tsarin miƙa ƴanciranin ga wata ƙasa a matsayin abin da ya saɓawa doka ya kuma saɓawa yardar da duniya ke da shi ga Amurka wajen samun kariya daga dukkanin barazana. Mai shari’a Chutkan ta buƙaci gwamnatin Amurka ta yi…
Aƙalla Masallata 40 ƴan bindiga suka sace a wani masallachi da ke Gidan Turbe a ƙaramar hukumar tsafe ta jihar Zamfara da safiyar yau Litinin, harin da kai tsaye masu ruwa da tsaki ke ganin ya kawo ƙarshen yarjejeniyar sulhu tsakanin ƴan bindigar da mahukuntan jihar. A baya-bayan nan ne jihohin Katsina da Zamfara suka ƙulla yarjejeniyar sulhu tsakaninsu da ƴanbindigar da suka addabi al’ummar jihohin arewa maso yammacin Najeriyar. Masu sukar tsarin na yarjejeniyar sulhu tsakanin ƴan bindigar da mahukunta, na ganin tun farko tsagerun wanda aka bayyana su da ƴan ta’adda tun ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaba Muhammadu Buhari…
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar neman kujerar shugabancin Najeriya har sau 2 a shekarun 2019 da 2023 Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa babu alamun shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu zai iya magance matsalolin da suka dabaibaye jama’ar ƙasar musamman na yunwa da kuma talauci. Ɗan adawar Atiku Abubakar wanda ya bayyana yunwar da ke addabar jama’ar Najeriya a matsayin matsalar da sam bai kamata ace ta faru ba, musamman lura da halin ƙuncin da marasa ƙarfi ke ciki. A cewar Atiku, jama’ar Najeriya na cikin wani hali na matsi da ƙuncin rayuwa da sam bai kamata ace…