Wasu alƙaluma sun nuna yadda gwamnatin jihar Sokoto ta kashe kuɗin da ya kai naira biliyan 9 da miliyan 900 wajen sayen motoci na alfarma adadin da ke matsayin kusan rabin kuɗaɗen shigar da jihar ta samu a shekarar 2024. Wannan na zuwa a dai dai lokacin da jihar ta yankin arewa maso yammacin Najeriyar ke fama da tarin matsaloli kama daga baƙin talaucin da ya addabi jama’arta da kuma ƙarancin ruwan sha da ake fama da shi dama lalacewar asibitoci koma ilahirin ɓangarorin kula da lafiya duk kuwa da ƙalubalen lafiyar da ake fuskanta. Kamar yadda ya ke ƙunshe…
Author: EDITOR
Antoni Janar na Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Yamai ya ce ’yan sanda suka fara binciken wanda aka fara kan wani yunƙurin kashe mutane a wata unguwa da ke wajen birnin Yamai, wanda ya kai ga kama wanda ake zargi da aikata laifin. Antoni Janar na Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Yamai a yayin wani taron manema labarai a ranar Lahadi ya bayyana cewa an kama tsohon minista Ibrahim Yacoubou bisa zarginsa da kashe mutane domin yin tsafi da su. A cewar Maazou Oumarou, komai ya fara ne daga binciken ’yan sanda wanda aka fara a ranar 29 ga Yulin 2025, kan…
An tsinci gawar wata ɗalibar aji ɗaya a Jami’ar Taraba da ke Jalingo (TSU), a ranar Juma’a a cikin ɗakin saurayinta, lamarin da ya tayar da hankali daliban a jami’ar. Ɗalibar mai suna Comfort Jimtop, ’yar ƙaramar hukumar Takum ce, kuma tana karantar fannin koyon aikin jarida. Rahotanni sun ce bayan an gano gawarta bayan mazauna gidan suka tsere. Kakakin rundunar ’yansandan Jihar Taraba, ASP Leshen James, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce suna neman saurayin tare da sauran mazauna gidan da suka tsere. Ya ƙara da cewa ’yansanda za su gudanar da bincike domin gano gaskiyar abin da…
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ayyana dan majalisar dokokin Jihar Filato dake wakiltar mazabar Jos ta Arewa, Adamu Aliyu, a matsayin wanda take nema a ruwa jallo, bisa zargin hannu a wata badakalar kwangilar TETFund ta sama da Naira miliyan 73 Mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da umarnin, bayan hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta shigar da bukatar hakan. Takardun kotu da ta gani, wani ɗan kasuwa mai suna Mohammed Jidda ne ya kai korafi ga ICPC yana zargin cewa dan majalisar ya yi masa alkawarin taimakawa wajen samun kwangilar Naira miliyan…
Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta janye yajin aikin gargaɗi na kwana biyar da ta fara a daren ranar Juma’ar da ta gabata. Shugaban ƙungiyar, Dakta Tope Osundara, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya aika wa jaridar Punch da ake wallafawa a ƙasar a daren ranar Asabar 13 ga watan Satumbar, inda ya umarci mambobinsu da su koma bakin aiki a wannan Lahadi. Osundara, yace gwamnati ta biya musu wasu daga cikin buƙatunsu, tare kuma da alƙawarin duba sauran batutuwan da suke yajin aiki akan su, sai dai har kawo yanzu babu wani ƙarin…
Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci ƙasashen da ke cikin ƙungiyar Tsaro na NATO da su dakatar da cinikin mai da Rasha, sannan sun sanya takunkumi ga ƙasar, kafin Amurka itama ta bi sahu da irin na ta takunkuman. Shugaban na Amurka Donald Trump ya ce ƙasar a shirye ta ke ta sanya gagarumin takunkumi ga Rasha kan yakinta da Ukraine muddun ƙasashen da ke cikin ƙungiyar NATO su ka fara da sanya irin nasu takunkumin da kuma dakatar da sayen mai na ƙasar. Har ila yau, shugaba Trump ya kuma bukaci mambobin ƙungiyar ƙasashen da ke yankin tekun Atlantika,…
FBI ta sanya ladar dala dubu 100 kan duk wanda ya gano maharin da ya kashe Kirk Jami’an hukumar FBI a Amurka da ke jagorantar bincike kan kisan makusancin Trump Charlie Kirk da wani mahari ya yi, sun sanya ladan dala dubu 100 ga duk wanda ya bayar da bayanai kan maɓoyar maharin da ya kashe fitaccen ɗan siyasar mai ra’ayin ƴan mazan jiya. Tuni FBI ta fitar da wani hoto, kodayake fuskar wanda ake neman bata fita sosai ba, amma ta ce akwai gwaggwaɓan lada kan duk wanda ya bayar da masaniya kan maharin. A Larabar da ta gabata…
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMet ta yi hasashen samun mamakon ruwa sama haɗa da tsawa har na tsawon kwanaki 3 a sassan Najeriya tun daga yau Juma’a har zuwa Lahadin makon nan. Hasashen masana yanayi da hukumar ta NiMet ta fitar jiya Alhamis a Abuja, ta ce wasu sassa na jihohin Kebbi da Sokoto da Zamfara da Kaduna da Kano da kuma Katsina baya ga jihar Taraba za su ga matsakaicin ruwa haɗe da tsawa a safiyar yau Juma’a. NiMet ta ce za a samu yayyafi da gajimare mai yawa a wasu sassa na jihar Neja da Kogi…
Alƙaluman waɗanda ke kamuwa da cutar Ebola a Congo ya ƙaru da fiye da ruɓaye guda cikin mako guda da sake samun ɓullar annobar cutar Lardin Kasai na kudancin jamhuriyyar Congo. Hukumar lafiya ta Afrika ta ce akwai fargaba matuƙa kan saurin yaɗuwar wannan cuta duk da matakan da mahukuntan ƙasar ke ɗauka. Cibiyar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta CDC ta ce daga adadin masu ɗauke da cutar 28 da ake dasu a farkon mako, adadin ya kai 68 a yanzu ciki har da wasu mutane 16 da cutar ta kashe. A cewar CDC yanzu haka akwai ɗimbin…
Wata gamayyar tsaffin kwamandojin hukumar Hisba a Kano sun zargi Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf da korarsu daga bakin aiki saboda matakinsu na ƙin amincewa da shiga jam’iyyar NNPP da ma rungumar tsari ko aƙidar Kwankwasiyya. A jihar ta Kano da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya, jam’iyyu biyu ke ci gaba da cin karensu babu babbaka, kuma su ne kan gaba wajen adawar siyasa da suka ƙunshi APC da NNPP. Da suke wannan zargi yayin ziyarar da suka kaiwa mataimakin shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Barau Jibrin a Abuja, jagoransu Alhaji Ahmad Kadawa ya yi iƙirarin cewa ba komai ne…