A ranar Talata, 9 ga Satumba, Isra’ila ta kai hari a birnin Doha, babban birnin Qatar, inda ta nufi wani jigo a shugabancin Hamas. Wannan hari ya haifar da rushewar shirye-shiryen tsagaita wuta da Amurka ke jagoranta a Gaza, wanda Shugaba Donald Trump ke kokarin cimmawa. A cewar rahotanni, harin ya kashe a kalla mutane shida, ciki har da wasu jami’an Hamas masu matsayi a ƙasa da ƙasa da kuma wani jami’in tsaron Qatar. Qatar, wadda ke da alaƙa mai ƙarfi da Amurka kuma tare da babban sansanin sojojin Amurka a Al-Udeid a ƙasar ta fusata akan wannan hari, inda…
Author: EDITOR
Kamfanin matatar mai ta Dangote zai fara shirin jigilar man fetur kyauta daga ranar Litinin mai zuwa, daga rahoton jaridar Punch. Mai magana da yawun rukunin kamfanin Dangote, Anthony Chiejina, ya bayyana a cikin sanarwar cewa shirin zai fara ne daga jihohin Kudu maso Yamma, Kwara, Delta, Rivers da Edo tare da babban birnin tarayya Abuja Ya kara da cewa matatar man ta riga ta rage farashin man fetur zuwa Naira 841 a kowace lita a Lagos da sauran jihohin Kudu maso yamma, yayin da a Abuja, Edo, Kwara, Rivers da Delta za a sayar da shi kan Naira 851 a…
Gwamna Abba Kabir Yusuf buƙaci majalisar dokokin jihar ta haramta abubuwan da suka shafi auren jinsi a jihar. Abba Kabir Yusuf ya buƙaci matakin hakanne bayan taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar ranar Laraba. Cikin ƙudurorin da majalisar zartarwar ta aike wa majalisar dokokin – wanda kwamishina Abduljabbar Mohammed Umar ya sanya wa hannu, ta buƙaci da majalisar ta amince da bukatar gwamnatin jihar na ɗaukar mataki tare haramta duk wani abu da ya shafi auren jinsi a a faɗin jihar. Jihar Kano da ke arewacin Najeriya na daga cikin jihohin ƙasar da ke amfani da shari’ar addinin musulunci…
Rukunin farko na ƴan ciranin Afrika sun isa Ghana daga Amurka, wanda ke ƙunshe da ƴan ƙasashen Najeriya da Gambia da kuma sauran yankunan yammacin Afrika. Wannan na zuwa ne bayan da tun a jiya Laraba shugaba John Dramani Mahama na Ghanar ya sanar da shirin fara karɓar ƴan ciranin amma bisa sharaɗin kasancewarsu ƴan ƙasashen yammacin Afrika kaɗai. Kafar labarai ta Reuters ta ruwaito cewa ƴan ciranin su 14 tuni suka sauka a birnin Accra yayin da mahukuntan ƙasar zasu taimaka wajen aikin rarrabasu zuwa ƙasashen su na asali. Shugaba John Dramani ya bayyana cewa tun farko Amurka ce…
Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da gano wasu ma’aikatan lafiya na bogi fiye da 100 a sassan jihar waɗanda ta sha alwashin ladabtar da su don kaucewa faruwar hakan anan gaba. Shugaban hukumar kula da asibitoci ta jihar Bauchi, Mr Sambo Alkali da ke bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da hukumar ta shirya yau Alhamis, ya ce nan gaba kaɗan za su miƙa sunayen waɗannan ma’aikata na bogi ga Gwamna Bala Muhammed don yanke matakin da za a ɗauka akansu bisa tanadin dokar ma’aikata ta jihar. A cewar Mr Sambo Alkali za su gabatar da wasu sabbin tsare-tsaren…
Kotu a Afrika ta kudu ta aike da wasu ƴan ƙasar China 7 gidan yari na shekaru 20 kowannensu bayan samunsu da laifin safarar mutane da kuma azabtar da su ta hanyar tilasta musu ayyukan bautarwa masu wahala. Ƴan Chinar da suka ƙunshi Maza 4 da mata 3, tun a farkon shekarar nan ne aka kame su tare da fara tuhumarsu da wannan laifi a gaban kotun ta Afrika ta kudu gabanin tabbatar da hannunsu dumu-dumu da ya kai ga yanke musu hukuncin. Bayanai sun ce mutanen da ƴan Chinar suka yi safararsu sun ƙunshi wasu ƴan ƙasar Malawi 91…
Kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin duniya zai yi zama kan harin Isra’ila a Qatar Kowanne lokaci a yau Alhamis kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin duniya ke shirin yin wani zama na musamman don tattaunawa kan harin da Isra’ila ta kai Qatar da nufin kisan jagororin ƙungiyar Hamas. Yayin wannan zama na kwamitin tsaron majalisar wanda Korea ta kudu ke jagoranta a yanzu, mambobin majalisar za su tafka muhawara kan harin na Isra’ila kan Qatar wanda Doha ta bayyana da keta dokokin ƙasa da ƙasa. Harin na ranar Talata ya faru ne lokacin da ake tsaka da tattaunawa kan ƙoƙarin cimma…
Ƙungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa ta NARD a Najeriya na duba yiwuwar tsunduma yajin aikin gargaɗi daga gobe juma’a 12 ga watan Satumba, bayan da ta baiwa gwamnatin ƙasar wa’adin sa’o’i 24 ƙari kan wa’adin kwanaki 10 da ta bayar tun a baya wanda ke kawo ƙarshe a yanzu. NARD ta cimma wannan mataki ne yayin taron majalisar zartaswarta a jiya Laraba, gabanin fitar da sanarwa a safiyar yau Alhamis kan yiwuwar tsunduma yajin aikin. Wannan ne karo na 3 da ƙungiyar ke bayar da wa’adi ga gwamnatin Najeriyar da nufin samun jituwa don kaucewa tsunduma yajin aikin wanda a…
Kwamandojin ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru sun gurfana gaban kotu a Abuja Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya ta sanar da gurfanar da wasu manyan kwamandojin ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru a gaban babbar kotun Tarayya da ke Abuja fadar gwamnati, waɗanda za su fuskanci mabanbantan tuhume-tuhume masu alaka da ta’addanci. Manyan kwamandojin biyu na Ansaru an bayyana sunayensu da Mahmud Usman wanda aka fi sani da Abu Bara’a Abbas ko kuma Mukhtar tare da mataimakinsa Mahmud Al-Nigeri da aka fi sani da Malam Mamuda. DSS ta gabatar da shafuka 32 na hujjojin da ta ke da su kan aikata…
Rwanda ta buƙaci Majalisar ɗinkin duniya ta yi watsi da koken maƙwabciyarta Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo da ke neman ayyana Kigali a matsayin wadda ta jagoranci kisan ƙare dangi a ƙasar ta hanyar ɗaukar nauyin mayaƙan M23 waɗanda har yanzu ke ci gaba da kashe-kashe a wannan ƙasa ta Afrika. A farkon shekarar nan ne mayaƙan na M23 waɗanda ke samun goyon bayan Rwanda suka kutsa gabashin Congo tare da ƙwace manyan garuruwa masu tasiri ga tattalin arziƙi da tsaron ƙasar. Wannan hare-hare na mayaƙan M23 ya kai ga kisan ɗimbin mutane kama daga fararen hula da kuma dakarun ƙasar har…