Wata fitacciyar mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam da Muhalli a jihar ribas tace Shugaba Tinubu baya jin tausayin mutanen jihar Ribas
A cewar Ann-Kio Briggs, shugaban kasa Bola Tinubu bai ji tausayin mutanen jihar Rivers ba game da ɗaga da dokar ta-baci da aka sanya a jihar na tsawon watanni shida.
A cewarta, an sanya dokar ta-baci saboda rikicin siyasa tsakanin tsohon gwamna Nyesom Wike da gwamna Siminalayi Fubara, wanda bai shafi jama’ar jihar ba.
Briggs ta ƙara da cewa mutanen jihar Ribas sun sha wahala a tsawon watanni shida ba tare da wani amfani ba, saboda hana gwamnati aiki yadda ya kamata.
Ta bayyana cewa Fubara yana da goyon baya mai karfi daga jama’a, musamman mata, amma dokar ta-baci ta kawo cikas ga ci gaba. Ta kuma ji shakkun yadda Tinubu ya kasance wani bangare na matsalar, saboda rashin adalci a cikin al’amarin.
A karshe, ta bukaci Fubara ya mai da hankali kan gudanar da mulki mai inganci don kawo ci gaba, amma ta jaddada cewa lokacin da aka rasa a lokacin dokar ta-baci dole ne a dawo da shi.
