Majalisar dattijan Chadi na gab da kaɗa ƙuri’a kan wani ƙudiri da ke tsawwaita wa’adin shugabancin ƙasar suwa shekaru bakwai-bakwai saɓanin biyar-biyar da ya ke a kundin tsarin mulkin ƙasar baya ga sahale shugaban ƙasar Mahamat Idris Deby damar neman wa’adi marar adadi.
Ƙar ƙashin wani ƙudiri da jam’iyya mai mulki ta MPS ta gabatar da nufin gyara a kundin tsarin mulkin cikin watan Disamban 2023, ya nemi sauya dokar da ke taƙaitawa shugaban damar riƙe muƙamin shugabancin wata ƙungiya ko jam’iyyar siyasa.
Tuni Majalisar wakilan Chadi ta aminta da wannan ƙudirin bayan kaɗa ƙuri’a da ya samu amincewa mambobi 171 yayinda ɗan majalisa ɗaya tal ya ƙalubalance shi.
Yanzu haka wannan ƙudiri ya isa gaban majalisar dattijai, wadda ke shirin kaɗa ƙuri’a kansa a ranar 13 ga watan gobe na Oktoba, a wani yanayi da bayanai ke cewa kashi 3 bisa 5 na mambobin majalisar dattijan na goyon bayan wannan ƙudiri.
Idan har wannan ƙudiri ya zama doka kenan, shugaba Mahamat Idris Deby na da damar jan ragamar ƙasar a wa’adi marar adadi na shekaru bakwai bakwai.
Kakakin Majalisar wakilan ta Chadi Ali Kolotou, ya bayyana cewa amincewa da ƙudirin ba wai yana nufin sauyi ga kundin tsarin mulkin ƙasar ba, face nazari da kuma bayar da shawara kan abun da suke ganin ya dace.
Bugu da ƙari wannan kudiri na neman gyara a kundin tsarin mulki ya kuma buɗe ƙofa ga yiwuwar samar da mataimakin Firaminista a wannan ƙasa ta yankin Sahel.
Wani batu da ke ƙunshe cikin wannan ƙudiri shi ne yadda ya ke neman cire rigar kariya ga ƙusoshin gwamnati ta yadda za a iya gurfanar da su gaban kotun gama-gari don fuskantar hukunci kan laifukan da suka aikata a bakin aiki.
A shekarar 2021 ne shugaba Mahamat Deby ya karɓi ragamar Chadi bayan mutuwar mahaifinsa Idris Deby Itno a fagen daaga wanda ya shafe shekaru fiye da 30 yana mulkar ƙasar.
