Darajar takardar kuɗi ta Najeriya Naira ta ɗaga a kasuwar musayar kuɗaɗen ƙetare yau Talata, inda ake sayar da kowacce dala guda akan ƙasa da farashin naira dubu 1 da 500.
Bayanai sun ce buƙatar tsabar takardar kuɗin ta naira ya sanya saukar farashin dalar wanda ya taimakawa asusun ajiyar kuɗaɗen ƙetare na Najeriyar wanda a ranar 11 ga watan nan ya kai dala biliyan 41 da miliyan 660.
Babban bankin Najeriyar CBN ya ce ana sayar da kowacce dala guda kan naira dubu 1 da 498 zuwa dubu 1 da 507, wanda ke nuna gagarumar nasara daga yadda aka faro sayar da dalar a farkon watan nan kan farashin dubu 1 da 526.
A kasuwannin bayan fage bayanai sun ce farashin kowacce dala guda na kaiwa Naira dubu 1 da 525 zuwa dubu 1 da 517.
