FBI ta sanya ladar dala dubu 100 kan duk wanda ya gano maharin da ya kashe Kirk
Jami’an hukumar FBI a Amurka da ke jagorantar bincike kan kisan makusancin Trump Charlie Kirk da wani mahari ya yi, sun sanya ladan dala dubu 100 ga duk wanda ya bayar da bayanai kan maɓoyar maharin da ya kashe fitaccen ɗan siyasar mai ra’ayin ƴan mazan jiya.
Tuni FBI ta fitar da wani hoto, kodayake fuskar wanda ake neman bata fita sosai ba, amma ta ce akwai gwaggwaɓan lada kan duk wanda ya bayar da masaniya kan maharin.
A Larabar da ta gabata ne maharin da har yanzu ba a gano aniyarsa ba, ya ɗirkawa Charlie Kirk alburushi a jijiyar wuya kuma nan take ya rasa ransa.
Sai dai FBI ta fitar da wasu faya-fayan bidiyo data tattaro daga kyamarorin tsaro waɗanda ke nuna lokacin da maharin ya shiga jami’ar ta Utah, tun gabanin fara jawabin Kirk, inda ya haye sama tare da neman wurin fakewa don aikata aika-aikar.
