Firaminista K.P Sharma Oli na Nepal ya yi murabus yau Litinin bayan matsin lamba daga matasan da suka shafe kwanaki suna jagorantar zanga-zangar adawa da matakinsa na kulle shafukan sada zumunta da suka ƙunshi Facebook da X da kuma YouTube.
Da safiyar yau Firaministan ya sanar da murabus ɗinsa, bayan da masu zanga-zangar suka tayar da hatta maganar rashawa da suka ce ta dabaibaye gwamnatin ƙasar ta yankin Himalaya.
Masu zanga-zangar waɗanda suka kai ruwa rana tsakaninsu da jami’an tsaro, har ya kai ga kisan mutane 17 bayan da ƴansanda a Kathmandu suka buɗe wuta kan masu zanga-zangar jiya Litinin wanda kuma ya kai ga jikkatar mutane 145 cikin har da jami’an tsaro 28.
Bayanai sun ce matasan da ke wannan bore sun ƙone majalisar dokokin ƙasar ta Nepal tare da wani ɓangare na gidan shugaban ƙasa dama wani sashe da filin sauka da tashin jiragen sama, wanda ya tialsta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama.
Tun farko gwamnatin Nepal ce ta gabatar da wani ƙudirin doka da ke neman bibiya tare da ɗaukar matakin magance taɓargazar da ake aikatawa a kafafen sada zumunta, dokar da bata yiwa matasan daɗi ba.
