Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da gano wasu ma’aikatan lafiya na bogi fiye da 100 a sassan jihar waɗanda ta sha alwashin ladabtar da su don kaucewa faruwar hakan anan gaba.
Shugaban hukumar kula da asibitoci ta jihar Bauchi, Mr Sambo Alkali da ke bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da hukumar ta shirya yau Alhamis, ya ce nan gaba kaɗan za su miƙa sunayen waɗannan ma’aikata na bogi ga Gwamna Bala Muhammed don yanke matakin da za a ɗauka akansu bisa tanadin dokar ma’aikata ta jihar.
A cewar Mr Sambo Alkali za su gabatar da wasu sabbin tsare-tsaren tantancewa don cire baragurbin ma’aikata a ilahirin asibitocin jihar.
Shugaban hukumar kula da asibitocin na jihar Bauchi, ya amsa cewa tabbas jihar na fama da ƙarancin likitoci wanda kuma matsala ce da ke addabar duniya baki ɗaya, kuma yanzu haka suna ƙoƙarin samar da likitoci fiye da 40.
A cewar shugaban hukumar Mr Sambo Alkali matakin da suka ɗauka yunƙuri ne magance manyan ƙalubalen da suka dabaibaye asibitocin jihar ta Bauchi.
Wannan ba shi ne karon farko da ake samun ma’aikatan bogi a sassa da hukumomin gwamnatin jihar ta Bauchi ba, wanda a lokuta da dama kan haddasa naƙasu ga tafiyar lamurran gwamnati.
