Shugaban hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta Najeriya FIRS Zacch Adedeji ya bayyana cewa kuɗaɗen shigar da suke tattarawa gwamnatin ƙasar ya ƙaru da kashi 411 cikin watannin baya-bayan nan sai dai duk da haka gwamnatin ƙasar za ta ci gaba da ciyo basuka don tafiyar da ayyuka.
Da ya ke amsa tambaya game da dalilin ci gaba da ciyo bashin, Mr Adedeji ya musanta cewa cin bashin nada nasaba da gazawar gwamnati, maimakon haka shugaban na hukumar FIRS ya ce basukan da ke kan Najeriyar manuniya ce ta ƙarfin tattalin arziƙi da kuma yadda gwamnati ke baza koma ko kuma faɗaɗa hanyoyin haɓaka tattalin arziƙinta.
Shugaban hukumar tattara kuɗaɗen shigar na Najeriya Mr Adedeji, ya ce a watan Satumban da muke na shekarar 2025 kuɗaɗen da Najeriyar ke samu sun ƙaru zuwa Naira tiriliyan 3 da miliyan ɗari 6 da 4 daga naira biliyan 711 da ƙasar ke iya tattarawa a watan Mayun 2023.
Hukumar ta FIRS ta ce yawan kuɗin da ake tattarawa a yanzu ya nuna yadda kuɗaɗen shigar na Najeriya ya ƙaru da kashi 411.
