Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya ce bai kamata wasubambance-bambancen da ke tsakanin ƙasarsa da Amurka su janyo rikicin soji ba.
Shugaban ya yi wannan jawabin ne jiya Juma’a yayin daAmurka ta aike da ƙarin jiragen yaƙi 10 zuwa Puerto Rico a kansojojin da aka jibge a ƙasar.
BBC ta rawaito Shugaba Maduro baya jin daɗin abin dashugaban Amurka ke yi wa ƙasarsa, kuma hakan ne ya sa ajiya ya ce yanzu kasarsa a shirye take ta tattauna kanabubuwan da Amurka ke buƙata.
Gwamnatin Trump ta ce tana murƙushe ƙungiyoyin ‘yandaba dake ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, waɗanda ya ce suna aika sucikin Amurka.
