Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMet ta yi hasashen samun mamakon ruwa sama haɗa da tsawa har na tsawon kwanaki 3 a sassan Najeriya tun daga yau Juma’a har zuwa Lahadin makon nan.
Hasashen masana yanayi da hukumar ta NiMet ta fitar jiya Alhamis a Abuja, ta ce wasu sassa na jihohin Kebbi da Sokoto da Zamfara da Kaduna da Kano da kuma Katsina baya ga jihar Taraba za su ga matsakaicin ruwa haɗe da tsawa a safiyar yau Juma’a.
NiMet ta ce za a samu yayyafi da gajimare mai yawa a wasu sassa na jihar Neja da Kogi da kuma Benue, yayinda wasu sassan kuma na jihohin Bauchi da Gombe da Adamawa da Taraba da Kaduna da Kano da Zamfara da kuma Katsina da Sokoto baya ga Kebbi za su ga makamancin yanayin, amma da ruwa mai ƙarfi.
Hukumar ta kuma bayyana fargabar fuskantar ambaliya sakamakon mamakon ruwan a wasu sassa na jihohin Lagos da Ogun da Akwa Ibom da kuma Cross River States.
Hukumar ta yi gargaɗi kan tuƙi a cikin yanayin na ruwa mai ƙarfi da wasu jihohin zasu fuskanta cikin wannan kwanaki 2, haka zalika ta buƙaci manoma su kaucewa zuba taki a gonaki gabanin lura da asarar da hakan zai kasance.
Bugu da ƙari hukumar ta NiMet ta buƙaci jama’ar Najeriya su kaucewa zama a yankunan da zasu iya fuskantar matsala ciki har da gidajen da ke gab da rushewa da kuma bishiyon da ka iya karyewa.
Haka zalika hukumar mai kula da yanayi a Najeriya ta buƙaci kamfanonin jiragen sama su samu cikakkun bayanai kan yanayin kowacce jiha daga jami’an filin jirgi gabanin kama hanya.
