Jam’iyyar PDP reshen Jihar Jigawa ta yi Allah-wadai da dakatar da Sule Lamido daga Kwamitin Amintattu na jam’iyyar (BoT), inda ta bayyana matakin a matsayin rashin adalci tare da neman a janye shi nan take.
Idan za’a iya tunawa dai kwamitin amintattu (BoT) na jam’iyyar PDP ya sanar da dakatar da Sule Lamido bisa zargin aikata ayyukan da suka sabawa ka’idojin jam’iyya da kuma kalamai masu tayar da zaune tsaye a yayin rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyar a baya-bayan nan.
Matakin ya haifar da ce-ce-ku-ce a cikin jam’iyyar lamarin da ya ƙara zurfafa rarrabuwar kai a jam’iyyar PDP reshen jihar Jigawa, tare da janyo kiraye-kirayen neman haɗin kai sakamakon fargabar samun koma baya a zaɓuka masu zuwa.
Da yake mayar da martani kan dakatarwar, a cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar PDP na jihar Jigawa Babandi Gumel ya fitar, ya bayyana matakin a matsayin rashin adalci tare da cewa ya janyo damuwa.
Babandi Gumel ya ce dakatarwar, wadda aka ce ta samo asali ne daga zargin cewa Lamido ya halarci wasu taruka da ka iya kawo barazana ga haɗin kan jam’iyyar.
“Bin haƙƙin doka da na kundin tsarin mulki a cikin jam’iyya ba za a iya fassara shi a matsayin aikin rarrabuwar kai ba,” in ji Gumel.
Ya tunatar da cewa Lamido ya nemi mafita ta shari’a ne bayan an hana shi damar sayen fom domin tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar na ƙasa.
“A kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci a amfaninsa, inda ta hana jam’iyyar PDP ci gaba da babban taronta na ƙasa har sai an tantance haƙƙin Lamido na tsayawa takara,” in ji shi.
Gumel ya bayyana dakatarwar a matsayin gaggawa da son zuciya, yana mai cewa hakan raina tsarin shari’a ne kuma ya yi kama da yanke hukunci tun kafin kammala bincike.
Babandi ya kuma bayyana cewa kundin tsarin mulkin PDP bai amince da dakatar da mamba na dindindin na, wato (life member) kamar Lamido ba, wannan ya buƙaci kwamitin amintattun ya janye dakatarwar nan take kuma ba tare da wani sharaɗi ba.
