Karamar Hukumar Karaye ta kaddamar da shirin dasa bishiyu iri daban-daban ga al’ummar yankin.
Babban Daraktan Kudi da Gudanarwa na Karamar Hukumar Karaye, Alhaji Abdu Mahmuda Doguwa, ya jagoranci bikin a madadin shugaban karamar hukumar, Alhaji Haruna Safiyanu Karaye.
Ya kuma yi karin haske kan muhimmancin bishiyu wajen rage kwararowar Hamada da kuma samar da tsaftataccen muhalli.
A nasa jawabin, shugaban sashin noma da albarkatun kasa na Karamar Hukumar Karaye, Malam Mai Kudi Abdu Kiru, ya bayyana cewa gwamnati ta raba bishiyu dubu goma (10,000) ga al’umma, wadanda suka hada da Darbejiya, Rimi, Madaci, Dogon yaro, Dorawa, da sauran su.
Sanarwar da jami’in yada labarai na karamar hukumar Karaye Abdullahi Sabo Muhammad ya firar tace taron ya samu halartar kafatanin shugabanin karamar hukumar da kuma sjhugabannin gargajiya dama kungiyoyin fafaren hula da sauransu.
