A ranar 10 ga Satumba, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, karkashin jagorancin Alkali Emeka Nwite, ta ki amincewa da belin wasu mutane biyar da ake zargi da shirya harin ta’addanci a ranar 5 ga Yuni, shekarar 2022, a Cocin St. Francis Catholic Church da ke Owo, Jihar Ondo.
Harin, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 40 da kuma raunatar mutane sama da 100, ya hada da wasu ‘yan bindiga dauke da bindigogin AK-47 da na’urorin fashewa (IEDs) wadanda suka kai hari a cocin a lokacin ibadar ranar Fentikos, inda suka buɗe wuta kan harbi masu ibada, sannan kuma tare da garkuwa da wasu.
Masu gabatar da kara sun ce kungiyar ta gudanar da tarurruka na shirin kai hari a watan Mayu da Yuni na shekarar 2022 a wurare kamar Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Ogamirana, Karamar Hukumar Adavi a Jihar Kogi, da kuma bayan Masallacin Omialafa a Karamar Hukumar Ose a Jihar Ondo.
