Kotun Amurka ta ɗaure wani babban jami’in NNPC kan laifin rashawa
Amurka ta damƙe wani tsohon babban jami’in kamfanin mai na Najeriya Paulinus Okoronkwo bayan samunsa da laifin karɓar rashawar dala miliyan 2 da dubu 100 daga wani kamfanin mai na China.
Bayanai sun ce Mr Okoronkwo ya karɓi waɗannan kuɗaɗe ne lokacin da ya ke bakin aiki a kamfanin man na Najeriya NNPC don baiwa kamfanin na China lasisin samun damar haƙar mai a cikin ƙasar ta yankin yammacin Afrika.
Bayan gurfana gaban kotu a Amurkan, Mr Okoronkwo mai shekaru 58 wanda lauya ne da yanzu haka ke zaune a birnin Los Angeles tuni ya amsa wannan tuhuma ta karɓar cin hancin maƙuden kuɗin.
Baya ga wannan tuhuma ta karɓar cin hanci daga kamfanin China, kotun a Amurka ta kuma samu Mr Okoronkwo da ake yiwa laƙabi da Pollie da wasu ƙarin laifuka har guda 3 ciki har da halasta kuɗaɗen haram da kaucewa biyan haraji baya ga hana doka yin aikinta.
Masu shigar da ƙara a Amurka sun ce Mr Okoronkwo wanda ke da shaidar zama a Amurkan ya karɓi kuɗaɗen ne tun a shekarar 2015 lokacin da ya ke matsayin babban manajan shiyya a kamfanin na NNPC.
