Wata gamayyar tsaffin kwamandojin hukumar Hisba a Kano sun zargi Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf da korarsu daga bakin aiki saboda matakinsu na ƙin amincewa da shiga jam’iyyar NNPP da ma rungumar tsari ko aƙidar Kwankwasiyya.
A jihar ta Kano da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya, jam’iyyu biyu ke ci gaba da cin karensu babu babbaka, kuma su ne kan gaba wajen adawar siyasa da suka ƙunshi APC da NNPP.
Da suke wannan zargi yayin ziyarar da suka kaiwa mataimakin shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Barau Jibrin a Abuja, jagoransu Alhaji Ahmad Kadawa ya yi iƙirarin cewa ba komai ne ya haddasa korarsu daga bakin aiki ba face siyasa.
A cewar Kadawa da ya ke jawabi gaban ɗan Majalisar, dukkaninsu za su nuna cikakken goyon baya ga jam’iyyar APC, yayinda mataimakin shugaban Majalisar Barau Jibril ya nuna rashin jin daɗinsa da wannan mataki tare da umartarsu da su kasance masu haƙuri.
Jihar ta Kano na sahun jihohin Najeriya da lamurra da dama suka juye siyasa, ta yadda kowacce gwamnati da ta zo ke tafiya da iyakar waɗanda ke mara mata baya tare da ajje waɗanda ke adawa da ita.
Masana na ci gaba da gargaɗi kan fifita siyasa a matsayin babban dalilin da ke ci gaba da gurgunta lamurran gwamnatocin jihohin arewacin Najeriya waɗanda ke matsayin koma baya tsakanin takwarorinsu na kudanci.
