A jiya da misalin da misalin ƙarfe 6 da minti 50 shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya Sauka filin jirgin saman Namadi Azikwe dake Abuja,
Shugaban ƙasa Tinubu ya tafi Birtaniya da kuma Faransa a ranar 4 ga watan Satumba a matsayin hutun shekara, sai dai mai magana da yawun shugaban ƙasa a kafar sada zumunta Bayo Onanuga ya sanar da cewa shugaban zai dawo ƙasar.
Sai dai a wani ɓangaren ana zaton cewa wa’adin dakatarwar da akayi wa gwamnan jihar ribas ya zo ƙarshe inda ake tunanin shugaban ƙasar zai janye dakatarwar a ranar Alhamis.
A ranar 18 ga watan Maris shugaban ƙasa ya sanya dokar ta ɓaci a jihar ribas biyo bayan hatsaniyar siyasa dake tsakanin gwamnan jihar da tsohon Gwamnan kuma ministan birnin tarayya Abuja, inda shugaban ya ɗauki matakin dakatar da shi tare da yan’majalissun jihar na tsawon watanni 6.
Shugaban ƙasa Tinubu ya ɗauki matakin hakanne ta hanyar bawa tsohon shugaban sojin ruwa Ibok-Ete Ibas rikon kwarya.
