Nan gaba Tinubu zai iya ciwo bashi daga Opay- Dino Melaye
Fitaccen ɗan siyasar Najeriya kuma tsohon Sanata da ya nemi kujerar Gwamnan jihar Kogi Dino Melayi ya yi kakkausar suka ga matakan gwamnatin ƙasar na ciwo bashi babu gaira babu dalili, yana mai cewa yanayin cin bashin da gwamnatin Bola Tinubu ke yi akwai yiwuwar a nan gaba da iya fara ciyo bashi da ƙananun cibiyoyin kuɗi da suka ƙunshi Opay da Moniepoint da sauransu.
Sanata Dino Melaye da ke wannan batu yayin zantawarsa da Arise TV jiya Litinin, ya gwada misali da yadda basukan ke ƙoƙarin yiwa Najeriyar katutu ƙarƙashin mulkin Tinubu wanda ya ce matakin na ci gaba da talauta talakawan Najeriyar.
Kalaman na Dino Melaye na zuwa bayan makamancinsa da shugaban Majalisar wakilan Najeriyar Abbas tajudden da ke cerwa ya zama wajibi ƙasar ta kawo ƙarshen basukan da take ci gaba da ciyowa haka suddan.
Wannan dai ne karon farko da wani ƙusa daga gwamnatin Najeriyar ke fitowa tare da sukar salon cin bashin na gwamnatin Tinubu ke yi.
Wasu alƙaluma sun nuna cewa a watanni ukun farko na shekarar 2024 ana bin Najeriyar bashin da ya kai naira tiriliyan 121 da biliyan 67 dai dai da dalar Amurka biliyan 91 da miliyan 406.
