NLC ta fusata da matakin Najeriya na ƙara albashin masu riƙe da muƙaman siyasa da kashi 114
Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya ta bayyana ɓacin ranta kan matakin gwamnatin Najeriya na ƙara albashin masu riƙe da muƙaman siyasa da kashi 114 cikin 100, wanda ke zuwa a dai dai lokacin da ɗimbin ma’aikata a sassa daban-daban ke kokawa da rashin kyawun albashi.
Shugaban ƙungiyar ƙwadagon ta NLC Joe Ajaero a wata sanarwa mai ɗauke dasa hannunshi ya bayyana cewa abin takaici ne matakin ƙara albashin da alawus alawus ga masu riƙe da muƙaman na siyasa dai dai lokacin da galibin ma’aikata ke kokawa.
Ajaero ya bayyana matakin rashin daidaito tsakanin ma’aikata da kuma nuna fifiko kan masu riƙe da muƙaman siyasan akan ma’aikata na haƙiƙa.
A wani yanayi da haraji ke ci gaba da yawa kan ƴan Najeriyar, rashin aiwatar da dokar mafi ƙarancin albashin ma’aikata na naira dubu 70, wasu ma’aikatan a matakan jihohi har yanzu basu samun hatta wancan mafi ƙarancin albashin na naira dubu 30.
Halin da ma’aikatan Najeriyar ke ciki ya sanya ɓangarori da dama bore inda aka riƙa ganin mabanbantan zanga-zanga kama daga ƙungiyoyin na ƙwadago da ma’aikatan ɓangaren lafiya da ma jami’an tsaro da uwa uba malaman jami’o’i.
Bayan kai ruwa rana ne gwamnatin Najeriyar ta amince da naira dubu 70 a matsayin mafi ƙarancin albashi amma bisa sharaɗin gwamnatin bazata ƙara farashin man fetur, sai dai jim kaɗan bayan wannan ƙari da har yanzu jihohi da dama basu aiwatar ba, ƴan Najeriyar sun sake ganin tashin farashin fetur wanda shi ke da alaƙa da hauhawar farashin kayaki da ke assasa tsadar rayuwa.
