Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar LP party ya babban tsokaci kan maganar da Dauda Lawan yayi akan jami’an tsaro inda ya bayyana hakan a shafin sa na X.
Yana mai cewa, “na karanta koken gwamnan jihar zamfara Dauda Lawal, ya bayyana cewa zai nuna duk inda yan bindiga suke a cikin daji amma kuma jami’an tsaro suna ansan umarnin ne daga Abuja kawai wanda kuma hakan na iya sa yan’ƙasa su cire yardar su akan shugaban ci”
Ya ƙara da cewa “rashin iko ga hukumomin tsaro na jihar na ƙara dagula lamarin tsaro a faɗin ƙasar tare da yiwa tsarin mulki kama-karya.
Peter Obi ya ƙara da cewa ba iya gwamnan jihar Zamfara ba, duk sauran gwamnonin dake buƙatar jami’an tsaron dole ne gwamnatin tarayya ta basu, domin kare rayukan yan’ƙasa.
Rashin yin hakan tamkar cin amanar mutane ne.
