Poland ta kakkaɓo jirage marasa matuƙa da Rasha ta harba mata
Poland ta sanar da harbo wasu jirage marasa matuƙi mallakin Rasha a sararin samaniyarta, karon farko da ƙasar mamba a ƙungiyar tsaro ta NATO ke ganin irin wannan takala daga Moscow, a wani yanayi da har yanzu ake ci gaba da kai ruwa rana tsakanin Ukraine da Rashan a ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙinsu na fiye da shekaru 3.
Firaminista Donald Tusk ya ce wannan ce mafi ƙololuwar takala da ƙasar ke gani daga Rasha inda dakarunta suka lissafa jirage marasa matuƙa har guda 19 da suka ratsa sararin samaniyarta, inda suka yi nasarar harbo guda 4 daga ciki.
Shugabannin ƙasashen Turai a sanarwar da suka fitar da ke kakkausar suka ga wannan hari, sun ce matakin na Rasha kai tsaye zagon ƙasa ne ga fatan da ake na kawo ƙarshen yaƙinta da Ukraine ƙarƙashin jagorancin shugaba Donald Trump na Amurka.
Sai dai Tuni Rasha ta yi watsi da wannan zargi, inda babban jami’in ofishin jakadancinta a Warsaw Andrei Ardash ke cewa babu wata hujja da ke nuna cewa Rasha ce ta harba jiragen suke hasalima ƙasar bata da aniyar faɗaɗa mamayarta zuwa Poland.
Poland na cikin ƙasashen mambobin ƙungiyar tsaro ta NATO wanda ke nufin kai mata hari tamkar takalo dukka mambobin wannan ƙungiya ne ta yadda kowacce zata iya ɗaukar mata fansa ciki har da Amurka.
A jawabinsa gaban zaman majalisar Poland, Tusk ya ce bashi da wani dalili da zai yi iƙirarin cewa suna gab da shiga yaƙi sai dai Rashan ta ƙetara dukkanin iyaka.
Firaministan na Poland, ya bayyana cewa halin da ake ciki a yanzu na ƙoƙarinsu kaisu kusa da yanayin da suka tsinci kansu gabanin yaƙin duniya na 2.
Sai dai Belarus a martaninta kan wannan hari ta ce tun farko jirage marasa matuƙan sun yi ɓatan hanya ne, da ta kaisu Poland maimakon isa inda suka nufa.
